Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ziyarci waɗanda harin ƙunar baƙin wake da aka kai garin Gwoza a Jihar Borno, ya rutsa da su.
A yayin ziyarar, Shettima ya bai wa waɗanda suka jikkata tallafi, tare da jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu.
- Lauyoyi mata sun nemi a kafa kotun sauraren shari’ar cin zarafi
- An soke aikin gyaran titi da aka ba kamfanin Dantata & Sawoe
Aƙalla mutum 18 ne aka ruwaito cewar sun rasu a lokacin da wasu ‘yan ƙunar baƙin wake huɗu suka tayar da bama-bamai a Gwoza a ranar Asabar.
Harin na baya-bayan nan ya haifar sa ruɗani a Jihar Borno, inda masu ruwa da tsaki suke ganin ana ƙoƙarin dawo da hannun agogo baya.
Mutane da dama sun ji rauni, inda wasu suka samu raunukan karaya, wasu kuma suka samu rauni a sassan jikinsu.
A ranar Litinin, Shettima ya bayyana cewa adadin waɗanda suka mutu a harin bam ɗin ya kai 32.
Ya ce an kai mutum 42 asibitin ƙwararru, amma an sallami 14 daga cikinsu bayan ba su kulawa. Ya ce har yanzu ana kula da mutum 26.
Mataimakin shugaban ƙasar, ya samu rakiyar mataimakin gwamnan Jihar Borno, Umar Kadafur; Sanata Ali Ndume; Ministan Noma da Abinci, Abubakar Kyari; tsohon Jakadan Najeriya a ƙasar Sin, Baba Ahmed Jidda da sauran ma’aikatan gwamnati.