✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe basarake da ’yan sanda biyu a Imo

An shiga farautar wadanda suka aikata wannan mummunar ta’asa.

Wasu ’yan ta’adda sun kashe wani basaraken gargajiya da wasu ’yan sanda biyu da wani farar hula daya a mararrabar Ahiara da ke yankin Ahiazu na Karamar Hukumar Mbaise da ke Jihar Imo.

Wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da sabon kwamishinan ’yan sandan Jihar Imo, Danjuma Aboki, ya soma rangadi tare da jami’ansa a karamar hukumar.

Aminiya ta samu cewa ajali ya katse hanzarin ’yan sanda ne a lokacin da suke bakin aiki sanye kakin dan sarki.

Haka kuma, bayanai sun ce karar kwanan ce ta cimma farar hular wanda tsautsayi ya biyo da shi hanyar kuma aka yi rashin sa’a harsashi ya same shi.

Shi kuwa basaraken gargajiyar da ya riga mu gidan gaskiya, shigar burtu ’yan ta’addan suka yi tamkar wasu baki masu kawo masa ziyara.

Kakakin ’yan sandan jihar, Henry Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa sun shiga farautar wadanda suka aikata wannan mummunar ta’asa.