✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

2023: Sanatoci na so a ba su takara kai-tsaye

Wasu daga cikin sanatocin na wakilatar mazabun gwamnonin jihohinsu, ga shi gwamnonin suna da kammala wa'adinsu na karshe, kuma suna neman maye gurbinsu a Majalisar…

Sanatocin jam’iyyar APC na rokon Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya tabbata sun samu tikitin komawa kujerunsu a zaben 2023.

Sanatocin sun yi kiran ne ganin yadda yawancinsu ke zaman doya da manja da gwamnonin jihohinsu, wanda hakan ke barazana ga yiwuwar su samu tikitin tsayawa takara domin komawa kan kujerunsu a babban zaben na 2023.

Sanatocin sun yi rokon ne a lokacin da Majalisar ke gudanar da zama bankwana ga Sanata ga Abdullahi Adamu wanda ya yi murabus bayan ya zama Shugaban Jam’aiyyar na Kasa tare da Sanata Abubakar Kyari wanda ya zama Mataimakin Shugaban Jam’iyyar daga Shiyyar Arewa sai kuma Sanata Hassan Muhammad Nasiha wanda shi kuma ya zama Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara.

Wasu daga cikin sanatocin na wakilatar mazabun gwamnoninsu, ga shi gwamnonin suna da kammala wa’adinsu na karshe, kuma suna neman maye gurbinsu a Majalisar Dattawa.

Da yake jawabi a lokacin taron, Sanata Ali Ndume ya koka kan yadda ake samun karancin sanatocin da ke dawowa kan kujerunsu.

Sanata James Manager daga jam’iyyar PDP a Jihar Delta ya bukaci  urged Adamu ya yi duk mai yiwuwa wajen kare ’yan majalisar da burinsu ta komawa kan kujerarsu ke fuskanatar “barazana”.

“Aikin farko da ke gabanka shi ne shi ne na kare wadannan ’yan majalisa, ba ni ba, tun da ba a jam’iyyarku nake ba.

“Ka san yadda ake yi, mun san ka mun kuma san abin da za ka iya, saboda haka muke so ka yi mana kokari yadda ya kamata,” inji shi.

Sanata Ndume ya ce a matsayinta na bangaren gwamnati, tana bukatar mutane masu gogewar da ta dace saboda abubuwan da ’yan Najeriya ke bukata daga gare su na da matukar girma.

Ya ce, “Amma yanzu tunda wasu daga cikin ’yan majalisar nan ne shugabannin jam’iyyar, akwai aiki a gabansu. Ba don mu ba, don majalisar.”

Da yake nasa jawabin, Sanata Abdullahi Adamu, ya ba wa majalisar tabbaci cewa sabbin mambobinta daga jam’iyyarsa ta APC za su kare martabar Majalisar Dokoki Ta Kasa yadda ya dace da tsare-tsaren jam’iyyar.

Abdullahi Adamu wanda ya bukaci sanatoci daga wasu kananan jam’iyyu su duba yiwuwar dawowa APC, ya ce, “Zan bar majalisa ne domin tunkarar wani aikin da na zaba wa kaina, wanda kuma zan tukare shi gadan-gadan.

“Akwai abokaina da nake fata tare da addu’ar cewa za mu ci gaba da tarayyar da muka dade muna yi da su.

“Wasu daga cikinku su ne mafiya nagartar mutanen da ake da su a kasar na, sai dai kuma kuna tare da bangaren da bai dace ba.”