Sanatan da ke wakiltar Katsina ta Arewa, mazabar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Majalisar Dattijai, Ahmed Babba-Kaita, ya koma koma jam’iyyar adawa ta PDP.
Rahotanni sun ce Sanatan ya mika takardar ficewarsa daga APC a matakin mazabarsa da ke Karamar Hukumarsa Kankiya, ranar Talata.
Ana ganin ficewar tasa ba ta rasa nasaba da tsamin dangantaka tsakaninsa da Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari.
A baya dai Sanatan ya sha sukar manufofin Gwamnatin Jihar da dama, musamman kan kin gudanar da Zaben Kananan Hukumomin tun bayan kafuwarta a 2015.
Rabon Katsina da zaben Kananan Hukumomi dai shekara bakwai ke nan, in ban da mako biyu da suka gabata.