Sanata Suleiman Othman Hunkuyi ya fice daga jam’iyyar PDP reshen Jihar Kaduna.
Sanata Hunkuyi shi ne ya wakilci mazabar Kaduna ta Arewa a Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2019 a jam’iyyar APC, ya sauya sheka ne bayan ya rasa kujerar takarar tasa.
- Rikicin Ukraine: Farashin gangar mai ya haura Dala 113
- Muhimman abubuwa 10 da ’yan Najeriya ke cewa a kan sabuwar dokar zabe
Bayanin ficewar tashi na dauke ne cikin wata sanarwa da ya fitar cewa, “Ina sanar da ku ficewata daga jam’iyyar PDP. Don haka ina so shugabanni su shaida hakan.”
Mun yi kokarin jin ta bakin Sanata Hunkuyi, amma hakarmu ba ta cim-ma ruwa ba.
Amma Sakataren Jam’iyyar PDP a jihar, Ibrahim Wosono, ya tabbatar mana da ficewar Hunkuyi daga jam’iyyar, wanda ya ce suna fatan hakan zai kawo wa jam’iyyar cigaba.
“Tabbas, mun samu takardar ficewarsa daga mazabarsa, don haka muna masa fatan alheri tare da samun nasara ga jam’iyyarmu,” a cewarsa.
Ya ce Sanatan ya jima da daina shiga harkokin jam’iyyar, don haka a cewarsa ficewarsa ba za ta shafi jam’iyyar ba.
Hunkuyi ya yi takarar kujerar gwamnan Kaduna a karkashin inuwar jam’iyyar PDP a 2019, amma ya fadi a zaben fidda-gwani.