✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sanata Barau ya jagoranci zaman Majalisar Dattawa

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Barau Jibrin ya shugabanci zaman Majalisar Dattawa na ranar Alhamis. Wannan dai shi ne karo na farko da ya jagoranci…

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Barau Jibrin ya shugabanci zaman Majalisar Dattawa na ranar Alhamis.

Wannan dai shi ne karo na farko da ya jagoranci zaman majalisar tun bayan buɗe ta ranar 13 ga Yunin 2023.

Sanata Barau ya shugabanci zaman majalisar ne kasancewar shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio bai samu halartar zauren ba.

Sanata Akpabio ya zama sabon shugaban Majalisar Dattawa

Barau Jibrin ya tsaya takarar shugabancin Majalisar Dattawa

Mataimakin shugaban ya shiga zauren tare da rakiyar ragowar jagogori inda aka fara zaman da misalin ƙarfe 11:00am.

Ya na zama kan kujerar shugabancin Majalisar kuma sai takwarorinsa sanatoci suka ɓarke da sowa da tafi.

Wakilinmu ya rawaito cewa Sanatan mai wakiltar Kano ta Arewa   ya jagoranci zaman majalisar cikin nutsuwa da walwala.