✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sanata Akpabio ya zama sabon shugaban Majalisar Dattawa

Sanata Godswill Akpabio ya kayar da abokin takararsa Sanata AbdulAziz Yari.

Sanata Godswill Akpabio ya lashe zaben shugaban Majalisar Dattawa.

An fara kada kuri’a ne da misalin karfe 08:45 na safiyar yau.

Sanata Godswill Akpabio da Sanata AbdulAziz Yari ne manyan ‘yan takarar da suka fafata a zaben, wadanda dukkaninsu daga jam’iyyar APC mai mulki suke.

An fafata ne tsakanin Yari, tsohon gwamnan Jihar Zamfara da Akpabio, tsohon Ministan Harkokin Neja Delta kuma tsohon gwamnan Jihar Akwa Ibom.

Akpabio da Yari su ne manyan jiga-jigan jam’iyyar APC da ke hankoron maye gurbin Sanata Ahmed Lawan.

Akpabio zai yi takarar da Sanata Barau Jibrin a matsayin mataimakinsa, yayin da Yari ya dauki Sanata Orji Uzor Kalu a matsayin nasa mataimakin.

Aminiya ta ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu dai tuni ya nuna goyon bayansa ga Godswill Akpabio domin zama sabon Shugaban Majalisar Dattawan.