Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya ce masu ikirarin cewa an yi cushe a Kasafin Kuɗin bana lissafi ne ya yi musu ƙaranci.
Wannan furuci na Shugaban Kasar na zuwa ne a matsayin caccaka ga Sanata Abdul Ningi na Mazabar Bauchi ta Tsakiya wanda a bayan nan ya yi ikirarin cewa an yi cushen da ya kai naira tiriliyan 3.7 Kasafin Kuɗin shekarar 2024.
- An yi wa mara lafiya dashen ƙodar alade a Amurka
- ‘Ana bai wa waɗanda ba su cancanta ba kwangiloli na miliyoyin Naira a Kano’
Tinubu dai ya yi caccakar ce a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin Majalisar Dattawan kasar a yayin wani zaman cin abincin buɗe baki a fadar gwamnati a ranar Alhamis.
Tinubu ya ce yana sane da duk wani lisaffi na jimillar kuɗin da aka kiyasta a Kasafin Kuɗin da ya gabatar wa Majalisar Dokokin da kuma ƙarin da ta yi bayan kammala nazari a kansa.
Dangane da hakan ne Shugaban Kasar ya ce duk masu ikirarin cewa an yi wani cushe ba su da fahimtar ilimin lissafi.
Ya ce gwamnatinsa ta tsaya kyam domin karfafa haɗin gwiwa da majalisar dokokin kasar wanda hakan zai kawo ci gaba a kasar nan.
Tinubu ya kuma bayyana cewa, mutuncin Majalisar Dokokin ba zai zube ba idon duniya a yayin da yake kuma miƙa godiyarsa dangane da goyon bayan da ’yan majalisar ke yi masa tun bayan hawansa mulki.
Dangane da batun kisan sojoji da ɓata-gari suka yi a Jihar Delta, Tinubu ya ce waɗanda suka yi aika-aikar za su fuskanci hukunci, yana mai gargaɗin cewa gwamnatinsa ba za ta amince da kai hare-hare kan sojoji da ababen more rayuwa ba.
“Rundunar sojojinmu na aiki tukuru, kuma ba za mu bar maharan su lalata mutunci da ƙimar sojojinmu da kuma shugabancinta ba.”