Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Abdul Ningi na tsawon watanni uku kan zargin cewa an yi cushen Naira tiriliyan 3.7 a Kasafin Kuɗin bana.
Aminiya ta ruwaito cewa hatsaniya ta soma kaurewa a zauren Majalisar Dattawan, yayin da sanatoci ke muhawara kan zargin cushe a cikin kasafin kuɗin ƙasar wanda shugaban ƙungiyar Sanatocin Arewa, Abdul Ningi ya yi a wata tattaunawa da sashen Hausa na BBC.
Tun da farko Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na majalisar, Sanata Olamilekan Adeola daga Jihar Ogun ya gabatar da ƙorafi kan tattaunawar da Sanata Ningi ya yi da manema labaran.
Ya soki lamirin kalaman Sanata Ningi wanda ke wakiltar Bauchi ta Tsakiya kan cewa ana amfani da Kasafin Kuɗi iri biyu a ƙasar.
Tun kafin hukuncin da majalisar ta ɗauka, Sanata Ningi wanda ya yi ƙoƙarin kare kansa, ya ce ba a fahimci kalaman nasa ba.
Bayan doguwar muhawara da Sanatoci suka yi kan lamarin, Sanata Jimoh Ibrahim na jam’iyyar APC mai wakiltar Ondo ta Kudu, ya ce a dakatar da Sanata Ningi na tsawon watanni 12.
Amma da yake bayar da tasa gudunmawa, Sanata Asuquo Ekpenyong mai wakiltar Kuros Riba ta Kudu ya roƙi a rage wa’adin hukuncin zuwa watanni 6.
Sai dai Sanata Sani Musa na jam’iyyar APC da Jihar Neja, ya ba da shawarar a dakatar da Ningi na tsawon watanni 3 sannan kuma ya rubuta wasikar neman gafara ga Majalisar Dattawan.
Bayan duk shawarwarin da suka bayar, Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio, ya ce, “an dakatar da Sanata Ningi na tsawon watanni uku kuma an cire shi daga dukkan ayyukan majalisar na tsawon watanni uku masu zuwa.”
Tuni dai Sanata Ningi ya rubuta takardar murabus a daga matsayinsa na Shugaban Ƙungiyar Sanatocin Arewa, yana mai miƙa godiyarsa ga mambobin ƙungiyar da suka ba shi damar jagoranci na tsawon watanni takwas.