Tsohon Sanata mai wakiltar Anambra ta Tsakiya a Majalisa Dattawa, Annie Okonkwo ya rasu.
Sanatan ya rasu ne a kasar Amurka yana da shekara 63, bayan ya sha fama da rashin lafiya.
- Rikicin Shugabanci: ’Yan sanda sun rufe majalisar dokokin Nasarawa
- Rusau: Tirela ta kashe yaro a wurin dibar ‘ganima’ a Kano
Okonkwo ya yi bikin cika shekara 63 a duniya a ranar 23 ga watan Mayu, 2023.
Babban dan kasuwa ne kuma dan siyasa daga yankin Ojoto a Karamar Hukumar Idemili ta Arewa a Jihar Anambra.
A baya ya kasance jigo a jam’iyyar PDP, daga bisani ya koma jam’iyyar APC mai mulki.
Lokaci na karshe da aka gan shi a bainar jama’a shi ne lokacin da dansa, Uche Okonkwo, ya samu tikitin tsayawa takarar majalisar dokokin a jihar.
A wani sako da ya wallafa a dandalin sada zumunta, sakataren watsa labarai na Anambra, Dokta Uche Nworah, ya ce: “Na farka ne da jin labarin rasuwar Agunaechemba (Sanata Annie Okonkwo).
“Agu mutumin kirki ne mai taimakon jama’a, kuma shi ne dan kasuwa na farko wanda ya zaburar da al’ummar Igbo da yawa ta hanyar kyawawan ayyukansa.
“Ina amfani da wannan dama wajen mika ta’aziyya ta ga iyalansa da daukacin jama’ar Anambra.”