✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Samar da ayyukan yi ba hakkin gwamnati ba ne —Fadar Shugaban Kasa

Kamfanoni masu zaman kansu ne za su samar da ayyukan yi.

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa samar da ayyukan yi ga ’yan kasa ba ya daga cikin hakkokin da suka rataya a wuyan gwamnati.

Mai bai wa Shugaban Kasa shawara kan harkokin yada labarai, Mista Femi Adesina, ya bayyana hakan ne ta cikin shirin ‘The Morning Show’ na gidan talbijin din Arise TV.

Furucin Mista Adesina na zuwa ne a lokacin da yake magana game da nasarorin da gwamnatin shugaba Buhari ta samu a cikin shekara takwas da suka gabata.

Adesina ya ce abin da kawai gwamnati za ta yi shi ne samar da kyakkyawan yanayi ga kamfanoni masu zaman kansu don su samar da ayyuka.

“Mafi yawan ayyukan da ake so ana samun su ne a kamfanoni masu zaman kansu.

“Matukar aka samu kyakkyawan yanayi, kamfanoni masu zaman kansu ne za su samar da ayyukan yi.”

Mista Adesina ya kuma ce gwamnatin Buhari ta cimma nasarori a bangarori da dama da suka hadar da bangaren mai da albarkatun iskar gas, da ayyukan more rayuwa da samar da dokoki da tsaro.