✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Tinubu ya taimaka wa ’yata ta samu aiki a NUPRC — Buba Galadima

Buba Galadima ya bayyana yadda 'yarsa ta yi aiki da gwamnatin Buhari na tsawon shekaru huɗu ba tare da an biya ta albashi ba.

Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana yadda Shugaba Bola Tinubu, ya taimaki ’yarsa ta samu aiki a Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Ƙasa (NUPRC).

Galadima, ya bayyana haka ne yayin wani shiri a gidan talabijin na AIT.

Ya ce duk da yana yawan sukar gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki, har yanzu shi da Shugaba Tinubu abokai ne.

Ya ce: “Abokai ne mu kuma za mu ci gaba da zama abokai. Idan ina buƙatar wani abu daga gare shi, zan iya tambayarsa.

“Bari na faɗi gaskiya a idon duniya. ’Yata ce ta yi amfani da wayata ta kira Shugaban Ƙasa, shi kuma ya yi zaton ni ne. Sai suka ce ’ya’yana ne, suka sanar da shi al’amura sun yi tsanani.”

Ya ƙara cewa: “Sun faɗa wa Tinubu cewa ‘mahaifinmu ba zai iya wannan ba, amma ya faɗa mana kai abokinsa ne.’

“Ɗaya daga cikinsu ta ce ta kammala NYSC amma ba ta samu aiki a NUPRC wacce Gbenga Komolafe ke jagoranta.

“Tinubu ya ‘kira Komolafe, ya ce ku bai wa ’yar abokina aiki.’ Shi ya sa ta ke son zuwa Makkah don yi wa Allah da Shugaban Ƙasa godiya.”

Galadima ya kuma bayyana cewa ’yarsa ta yi aiki a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari na tsawon shekara huɗu ba tare da an taɓa biyanta albashi ba.

Ya ce: “’Yata ta yi aiki da shi (Buhari) har na tsawon shekara huɗu, kuma ya bayar da umarnin kada a biya ta albashi.

“Sai dai duk wata a kawo takardar da ke nuna an biya ta. Ta yi aiki da Buhari shekara huɗu a ofishin Osinbajo ba tare da ta karɓi ko sisin kwabo ba,” in ji shi.

Galadima, ya kuma ce shi kansa ya yi aiki tare da Buhari na tsawon shekara goma sha uku.

Wannan kalamai sun bai wa mutane da dama mamaki, musamman ganin cewa Galadima ya shahara wajen sukar gwamnatin APC a fili.