Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun bayyana cewa aƙalla maniyyata miliyan 1,833,164 ne suka halarci aikin Hajjin 2024.
Kamfanin dillancin labaran Saudiyya, ya ruwaito cewar jimillar maniyyatan ƙasashen waje miliyan 1,611,310 da kuma maniyyata mazauna ƙasar 221,854 ne, suka gudanar da hajjin na bana.
- Mun soke da hawan sallah don wanzuwar zaman lafiya — Aminu Bayero
- Gobara ta lakume dukiya ta miliyoyin naira a Legas
Daga cikin maniyyatan akwai maza 958,137 da kuma adadin mata 875,027.
“Adadin maniyyatan da suka fito daga ƙasashen Larabawa ya kai kashi 22.3 cikin 100, yayin da adadin maniyyata daga ƙasashen Asiya ya kai kashi 63.3.
“Yawan maniyyata daga ƙasashen Afirka ya kai kashi 11.3 yayin da yawan maniyyata daga ƙasashen Turai, Amurka, Austaraliya da sauran ƙasashen da ba a tantance ba ya kai kashi 3.2.”
Hukumomin ƙasar sun bayyana cewa, akasarin maniyyatan sun isa ƙasar ne ta jirgin sama.
Alhazan ƙasashen waje da suka sauka a filayen jiragen saman Saudiyya sun kai 1,546,345 yayin da maniyyata 60,251 suka ƙasar ta ƙasa, sai mutum 4,714 suka isa ta tashar jiragen ruwa.
“Abin lura ne cewa GASTAT ta fitar da ƙididdigar bayanan Hajjin 2024, kuma ta dogara ne da bayanai daga majiya mai tushe. Sanarwar ƙididdigar Hajjin ta kasafta maniyyata kan tsarin bayanan jinsi, ƙasa da kuma hanyar da suka isa ƙasar,” in ji ta.