✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta lakume dukiyar miliyoyin naira a Legas

Babu rahoton rasa rai sai dai makwabtan da suka kai dauki sun samu kananan raunuka.

A safiyar ranar Juma’a ce aka samu rahoton tashin gobara wadda ta yi gagarumar ɓarna a wani katafaren gini da ke kan titin Alhaji Jubril na Magodo Phase II da ke Jihar Legas.

Gobarar da ta tashi daga ɗaya daga cikin gidaje biyu na ginin da lamarin ya shafa ta kuma lalata kadarori na miliyoyin naira.

Kodayake, babu rahoton rasa rai yayin da lamarin ya auku, sai dai wasu ganau sun bayyana cewa makwabtan da suka yi yunkurin kashe gobarar a lokacin da ta tashi sun samu kananan raunuka.

Babban Sakataren Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA), Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Da yake bayar da karin haske game da lamarin, Dokta Damilola ya ce hukumar ta amsa kiran gaggawar ta wayar tarho cewa gobara ta tashi a wani bene mai hawa daya da ke lamba 16 a titin Alhaji Jubril na unguwar Magodo Phase II.

Ya ce jami’an hukumar da kuma na cibiyar kula da bada agajin gaggawa da ke Alausa sun isa gidan da gobarar ta tashi da misalin karfe 8:02 na safe.

Ya kara da cewa, da isar su jami’ansu suka shiga aikin kashe gobarar wadda ta rika yaduwa daga babban dakin da ke dauke da dakunan kwana kusan biyar.