Matashin nan dan asalin Jihar Gombe da ya yi tattaki har zuwa Legas saboda tsohon Gwamnan Jihar, Bola Ahmed Tinubu amma ya kasa haduwa da shi bayan shafe kwana 25 ya ce sam bai yi nadama ba.
Matashin mai suna Aminu Abdulmumini Jor ya shaida wa Aminiya cewa ya fuskanci kalubale da dama a lokacin tattakin, kuma ya yi ne domin kaunar da yake wa Tinubun.
Ya ce, “Ina kaunarsa ne saboda dattakunsa da kwarewarsa wajen sha’anin gudanar da mulki, kuma na yi imanin shi ke da kwarewa da zai rike kasar nan ya kai ta ga gaci
“Na fara tattakin ne a ranar 24 ga watan Maris din 2022, kuma na isa Legas a ranar shida ga wata Afrilu.
“Kalubalen da na fuskantar bai wuce na rana da zafi ko yunwa da kishirwa ba, amma babban kalubalen shi ne yadda wasu mutane suka kalli tafiyar tawa suka yi ta min mugun fatan Allah ya hada ni da barayi ko masu garkuwa da mutane ko ’yan bindiga, amma Allah ya kiyaye ni, saboda kudirina mai kyau ne, kuma Allah yana kare mutum mutukar yana da kyakkyawar niyya.
“Na yi tafiyar ne ba dare ba rana, amma idan na ratso ta babban gari cikin dare nakan tsaya na kwana na ci gaba da tafiya da karfe 7:00 na safe, idan kuma a ƙauye na kwana, sai na yi asubanci da karfe 4:00 na ci gaba da tafiya.
“A lokacin tafiyar tawa, akasari abincina dabino ne da ruwa sai kuma madara, na kuma kashe kudin guzuri sama da Naira dubu 100 a lokacin tafiyar,” inji shi.
Ya ce bayan ya isa Legas ya je Ofishin Gwamnatin Jihar Legas ya kuma je gidan gwanin nasa, Tinubu, amma masu gadin gidan suka hana shi shiga.
“Ka san su masu gadin ba ’yan siyasa ba ne, aikin su suke yi na tsaro, sun hanani shiga, haka zalika akwai taron da aka shirya wa Tinubu a filin wasanni na Surulere nan ma na je amma ban sami ganawa da shi ba, sai dai na hange shi na kuma yi farin ciki sosai,” inji matashin.
Ya ce babban fatan shi shi ne wata ran Allah ya kaddara su yi ido hudu da gwanin nasa.