Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta shirya tsare-tsaren tsaro domin ganin an yi Sallar Idi cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.
Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa za a tura ’yan sanda da sauran jami’an tsaro zuwa filayen Idi, Masallatai, da wuraren taro domin kula da tsaro da zirga-zirgar jama’a.
- Ambaliyar Mokwa: An gano gawar yara 7, jama’a na neman agaji
- Kotu ta aike da ɗan Tiktok gidan yari kan yin shigar mata a Kano
Za a sanya ido sosai a manyan hanyoyi musamman waɗanda ke kai wa zuwa wuraren sallah, domin rage cunkoso da sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a.
An ware ƙofofin shiga da fita a filayen Sallah domin a riƙa duba mutane da kayan da suke ɗauke da su.
Rundunar ta kuma roƙi jama’a da su bi waɗannan ƙa’idoji domin kauce wa jinkiri.
’Yan sandan sun gargaɗi mutane da ka da su ajiye motoci ba bisa ƙa’ida ba, sannan su kaucewa yin salla a tsakiyar hanya, ko toshe hanyoyin fita.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, ya roƙi mutane da su bayar da haɗin kai wajen bin doka, tare da kasancewa masu lura da duk wani abu da zai kawo barazana.
Ya kuma gargaɗi masu laifi da su guji duk wani abu da zai jawo tashin hankali a jihar.
Hakazalika, ya taya al’ummar Gombe murnar Sallar Idi, tare da tabbatar musu cewa ’yan sanda za su ci gaba da kare lafiyar jama’a domin a yi bukukuwan sallah cikin kwanciyar hankali.