Ranar Sallah rana ce ta farin ciki da nuna godiya ga Allah bisa ni’imominsa da kammala azumin Ramadan lafiya.
Abubuwan da malamai suka kwadaitar a aikata da Karamar Sallah su ne:
- Wasu ’yan Izala sun bijire wa Sarkin Musulmi, sun yi Idi ran Laraba
- Wasu ’yan Izala sun bijire wa Sarkin Musulmi, sun yi Idi ran Laraba
- Ranar Alhamis za a yi Sallah — Sarkin Musulmi
- Yin kabbarori da zarar an ga watan Shawwal.
- Wankan idi kafin zuwa masallacin idi a ranar Sallah.
- Sanya sabbin kaya ko mafiya kyawunsu don zuwa idi.
- Yin ado da fesa turare (ga maza).
- Cin abinci kafin tafiya masallacin idi.
- Tafiya sallar idi a kan lokaci.
- Zuwa tare da mata da kananan yara.
- Yin kabbarori a bayyane yayin tafiya idi.
- Ba a yi wa sallar idi kiran sallah.
- Babu nafila kafin sallar idi ko bayanta.
- Yin sallar idi a bayan liman.
- Sauraron hudubar bayan sallar idi.
- Taya juna murna da fatan alheri.
- Sauya hanyar dawowa daga idi.
- Sadar da zumunci a lokacin idi.
- Bayar da kyaututtuka.