A Bikin Yawan Sallah na Jafi da aka yi a fadar Sarkin Gombe, Mai Martaba Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, ya yi kira ga manoma da makiyaya da su zauna lafiya da juna.
Sarkin ya ce zaman lafiya shi ne ginshiƙin ci gaba, kuma haɗin kai tsakanin manoma da makiyaya zai hana rikice-rikice da ke barazana ga jihar.
- Matashi ya kashe jami’in tsaron Sarki Sanusi II a Kano
- Gwarzon gasar Alƙur’ani ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga a Katsina
“Ina roƙon manoma da makiyaya da su zauna lafiya don guje wa rigingimu.
“Kowa yana da haƙƙin tabbatar da zaman lafiya domin hakan na kawo ci gaban tattalin arziƙi da walwalar al’umma,” in ji Sarkin.
Haka kuma, ya tabbatar da cewa masarautar Gombe za ta ci gaba da goyon bayan gwamnatin jihar domin tabbatar da tsaro mai ɗorewa.
Sarkin ya gode wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa ƙoƙarinsa na inganta rayuwar al’umma da ɗaukar matakan tsaro, musamman samar da motocin aiki ga jami’an tsaro.
Bikin hawan sallah na Jafi ya samu halartar manyan baƙi, ciki har da Gwamnan Jihar Gombe da wasu manyan jami’an gwamnati, inda aka jaddada buƙatar haɗin kai da zaman lafiya a jihar.