✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sallah: Hukumar sibil difens ta girke jami’ai 5,000 a Abuja

An gargaɗi duk wasu miyagu da su kiyaye muhimman kadarorin ƙasa da ababen more rayuwa.

An jibge ya jami’ai 5,112 na hukumar tsaron sibil difens domin ƙarfafa matakan tsaro a babban birnin ƙasar albarkacin bukukuwan Sallah da za a shiga nan ’yan kwanaki.

Kwamandan hukumar ta NSCDC shiyyar babban birnin tarayya Abuja, Dokta Olusola Odumosu na ya bayar da umarni kamar yadda wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau Alhamis.

Kakakin rundunar, Samuel Idoko ya ambato Odumosu na cewa dakarun da aka tura za su yi aiki ne a dukkan lungu da saƙo na ƙananan hukumomin shida da ke babban birnin kasar.

Ya kuma gargaɗi ɓata-gari da sauran miyagu da su kiyaye muhimman kadarorin ƙasa da ababen more rayuwa.

Ya jaddada cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kama wanda ya aikata laifi kuma doka za ta hau kan duk wanda aka kama ko aka samu da laifi.

Odumosu ya kuma yi gargaɗin a guji ƙona tayoyi a kan hanya domin hakan yana shafar ingancin hanyar da kuma ɓarnar dukiya, yana mai cewa duk wanda aka kama za a hukunta shi.

Kazalika, ya kuma jaddada yadda jami’an tsaro ke daɗa yaɗuwa a faɗin babban birnin kasar tare da ba da tabbacin cewa, duk wanda aka kama yana aikata irin waɗannan laifuka zai girbi abin da ya shuka a gaban shari’a.