✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun haramta Hawan Sallah a Kano

Bana babu hawan Sallah a Kano saboda dalilai na tsaro a cewar rundunar ’yan sandan jihar.

Rundunar ‘yan sandan Kano ta haramta duk wasu haye-hayen Durbar da bisa al’ada aka saba gudanarwa a duk lokutan bukukuwan sallah a jihar

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

A bayan nan ne Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya gayyaci hakimai zuwa Durbar tare da neman ‘yan sanda su samar da tsaro a lokutan bukukuwan Sallah Babba da za a soma ranar Lahadi.

Sai dai a sanarwar da ta fitar, rundunar ‘yan sandan ta ce bana ta haramta duk wasu haye-hayen Sallah saboda dalilai na tsaro.

Ana iya tuna cewa a ranar 23 ga watan Mayu ne gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautun Kano ta 2024, bayan majalisa ta amince da ita.

Wannan ne ya bayar da damar komawar sarkin Kano na Muhammdu Sanusi II a matsayin sarkin Kano na 16 tare da cire Aminu Ado Bayero daga kan mulki.

Wannan lamari da yanzu haka ya kai har gaban kotu ya janyo ruɗani, inda Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II kowannensu ke iƙirarin shi ne halastaccen sarki.