Masana’antun Jigawa
Ku ba ni dama a wannan jarida mai Farin jini na yaba wa Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar , wanda a cikin wata biyu ya yi aiki da ya fi 20, wato a duk kwana biyu ya yi ayyuka uku.
Ina kuma ba da shawara a farfado da Masana’antar fulawa ta Gumel, kuma a yi masana antar man Ridi a Maigatari, da Masana’antar Tumatur akan kogin Hadeja; a kuma binciki ma’adanin yin gilashi a Kazaure, wanda aka ce akwai wadannan albarkatu da za su habaka arziki , su kuma samar da ayyukan yi ga matasa. Gaba dai, gaba dai, gaba dai Baba! Daga Hansa’u Hussaini Dauda Girbobo 08030453683.
Kira ga Ganduje
Edita ba zan gaji da aiko da sako b,a duk da ba a rubata sakona a jaridarmu. Sakona a gareku shi ne kira ga Maigirma Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da kada ya bari ’yan adawa su shiga tsakaninsa da mai gidansa sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Domin idan ka yi haka ka ci amana. Wasalam. Daga Aminin Aminiya Sani CK Madobi, Jihar Kano.
Kira ga Gwamna Masari
Assalamu alaikum. Aminiya ina son ku isar mani da sakona ga gwamnamu na Katsina, Aminu Bello Masari ya taimaka ya yi mana tagwayen hanya, daga kofar Sauri zuwa Shinkafi. domin hanyar ta yi kadan. A kalla tana cin sama da mutun 10 a shekara, saboda duk hanyoyin da ke Katsina, ba inda ake hadari kamarta. A taimaka, Allah ya taimakemu, amin. Daga Alhaji Salisu Shugaban dan Bekuta Blocks 07064844087
Ga Gwamna el-Rufa’
Edita ina mai matukar farin cikin karanta jaridarku mai albarka, jarida mar albarka, jarida kwaya daya tilo mai kare muradun “yan najeriya ba masu mulkinta ba. Edita sakona ga el-Rufa’i shi ne, idan ya gama rushe gidajen azzalumai, saura azzaluman da suka sayar musu da filayen su ma akamo su, domin su fuskanci hukunci. A kwato haramtacciyar dukiyar da take hannunsu azuba su a,asusun gwamnati domin yazama aya ga masu sha,awar aikata sake sayar da filayen gwamnati. Ina fatan gwamnati zata karbi shawarata. Daga sirajo muhammad paki mile 12 lagos 08034679768
Jinjina ga Buhari
Edita kabani dama najinjinawa janar buhari sabida nadinda yayiwa dan halak malak na buhari wato Hon.kawu sumaila amasayin mai bashi shawara akan harkokin majalirar tarayya wannan nadi yadace an dora kwarya a gurbinta mu kanawa muna godiya. Daga Abubakar Umar Kofa 08065746051.
Mulkin Buhari ya fi shekarar PDP 16
Aminiya, yar’ amana, don’ Allah, ku mika mana sako ga jam’iyyar PDP, cewa kwana 100 na shugabancin Buhari akan gadon mulki ya fi shekara 16 amfani a wurin talakawa, Domin yanzu muna barci da ido biyu, cin hanci ya ragu; farashin mai ya daidaita; wuta ta samu, duk a jagorancin Shugaba Muhamadu Buhari. Daga Musa da Rabi’atu, Unguwar Maiyasin, danja Jihar Katsina 08155648155,08069274090
Akwai sake
Asalamu alaikum. Masu bai kamata masu kwace hakki bil adama su ce a koya wa ’yan Boko Haram sana’a ba. Wa ya san abin da za su yi nan gaba. Bayan duban mutane da suka hallaka. Ibrahim Shehu Kacacare.
Kira ga matasa salam
Aminiya ku ba ni dama inyi kira ga matasa, don su kiyayi miyagun kwayoyi. Daga Aminu D. Kwamama.
Ga EFCC
Edita ka ba ni dama wallahi ba don rashin harshe ba, ba Jigawa ya kamata a bincika ba, amma rashin harshe zai iya haifar da komai. Mu ’yan Jigawa don uwar yaran zamani kowa ya iya bakinsa, ban da katobara. In karya nake ku tambayi lamuran duniya. 08063437074.
Ta’aziyya da jaje ga Saudiyya
Salam,editor abani damar meka ta’aziyya ta ga ‘yan uwa musulmi wadanda suka rigama mu gidan gaskiya a hadarin masallacin Haram dake saudiyya,ya ritsa dasu.Wadanda suka samu raunika kuma,allah ya basu lafiya.Ameen. Ha’ila yau inason a mika min jaje na ga Saudiyya akan iftila’in.Allah ya kara kare afkuwar irinsa.A kuma aika sako na ga hukumar tsaron Saudiyya cewa”anya ba ‘yan’Houthi’ne daga Yemen suka zo suka gotar da karfen ba kuwa? Allah ya kara kare al’ummar musulmin duniya baki daya. Ameen. Daga Aminu Muhammad Adamu, Nassarawa G.R.A,Kano. 08035914445.
Kira ga ’yan Arewa
Ina mamakin rashin hakuri irin namu. Wallahi ’yan Arewa mu sani matukar yaki ya ci Buhari, to wallahi ba shi ya ci ba, mu ya ci. Saboda haka wallahi mu kara dagewa da addu’a ba gaugawa ba. Idan muka yi hakuri za mu ji dadi da fatan Allah ya taimaki Baba Buhari ya kara masa lafiya da yawancin kwana. Amin,Daga dan uwanku Ibrahim B Ibrahim katsina 08061640383.
Ga Gwamna Tambuwal
Assalam aminiya hausa ku isar min da wannan sakon ga Maigirma Alhaji Aminu Waziri Tambuwal. Muna rokonsa da ya canza mana rijistar makarantar da ke Kwalejin Ilimi ta Sakkwato (College of Education Sokoto). Domin Allah. Daga Baban Jabiru (na Manzon Allah).
APC ga Jafaru Isa
Editan Aminniya ka ba ni dama in nuna farin cikina da nadin mai bayar da shawara kan majalisar kasa da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Alhaji Kawu Sumaila. Sannan ina tunatar da Jam’iyyar APC a Kano da kasa baki daya, cew3a, akwai sauran “Gwarzon Talakawa” Lawal Jafaru Isa, lallai akwai bukatar a ba shi mukamin da zai yi wa al’umma amfani. Tarihi ba zai manta da abin da ya yi wa al’umma a Jihar Kaduna ba, musamman kantin sauki na “KADA PAYLESS.” Bayan an karbo dukiyar al’uma da wasu suka kwasa, to a yi wa talakawa abin da zai amfane su. Allah Ya taimaki Gwamnatin APC da Shugaba Buhari. Daga Ahmad Tiga. 08068643445.