Malamai ne tushen gwamnati
Edita, hakika Ilimi ne gishirin zaman duniya, da ‘yan magana suke masa kirari da na zangi moriyar ka da nisa. Sai dai duk da muhimmancinsa, ba zai samu ba, sai ta hanyar malamai, tun daga matakin Firamare, da Sakandare zuwa Jami’a. Duk da muhimman cin malamai wajen bayar da ilimi ga dalibai, da za su kawo canji a cikin al’umma, suna fuskantar matsaloli da daman gaske, musamman a matakin Firamare, inda ba a biyan su hakkokinsu. Ina kira ga gwamnatin daga matakin tarayya, har zuwa karamar hukuma, da su inganta albashin ma’aikata, tare da daukar dawainiyar ba su horarwa ta musamman (Training) don koyar da dalibai, cikin hikima da fasaha, da za su samu ingantacce ilimin da zai kai su zuwa jami’a, don nazarin fannoni, da dama, musamman fannin kimiya da fasaha, dake tafiya dai-dai, da wannan zamani. Daga Aminu Dankaduna Amanawa. [email protected] 09035522212
Addu’a ga Sarkin Kano
Salam Edita ina maka fatan alhairi, tare da dukkan ma’aikatan wannan jarida tamu ta Aminiya, wacce muke alfahari da ita Edita ka ba ni dama in taya Maimartaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu SanusiII murnar hawan sallar da ya yi bayan ya dawo daga kasa mai tsarki. Abin murna da jin dadi sarkinmu ya yi hawa ne kan taguwa, maimakon kan doki, kamar yadda Kanawa muka sani. Ina addu’ar Allah kara wa sarki lafiya, ya jikan Sarki Sanusi na daya amin. Daga Muhd Ahmad Idris a Kabuga Kano 08031818318
Jinjina ga Jamila Kaugama
Edita ka mika mini jinjinata ga Hajiya Jamila Faruk Kaugama. Allah ya saka miki da alkhairi, kamar yadda kike taimaka wa jama’ar Jigawa da ma Najeriya mun gode. Daga Baban Nura Tela Sabon Garin ’Ya’ya, Taura, Jihar Jigawa
A sauke CRC a Kano
Assalamu alaikum.Babban Edita, muna kira ga sabon Gwamna Kano da ya sauke Hukumar CRC, saboda wallahi ni ban san ofis ko da na karamar hukumata ba. Makarantun da aka ce an zagaye mafi yawancin su na bakin titi ne. Kuma shugabancin hukumar gado ne; abincin yara karya ce; gidajen malamai karya ce a Firamare. Babu abin zama a ajujuwa. A binciki hukumar. Daga Babangida Ahmad Jibrin Zangon Dakwara Gwarzo
Kira ga Gwamna Masari
Edita ka mika kirana ga Gwamna Masari na Jihar Katsina, da ya taimaka ya yi mana hanyar mota daga Bakori zuwaTsiga zuwa Barde zuwa Kwantakwaramm zuwa Masari. Don hanyar ta zama tarkon mutuwa, kuma ga shi hanyar ta jamma’a ce, musamman ma manoma. Daga Usman Musa Kwantakwaram 07069718268
Addu’a ga Gwamnati
ASLM. Jama’a talakawan Najeriya da Jihar Katsina, ina kira garemu baki daya da mu ci gaba da yi wa wannan gwamnati irin addu’ar nan da muka rika yi lokacin da muke neman canji mafi alheri daga Allah. Mu tuna Allah muka ba zabi, Shi kuma Ya zabar mana wadannan shugabanni, ya kamata mu bi su da addu’ar alheri, sai Allah Ya shirya mana su, su kasance masu tausayin mu. Kada mu butulce wa Allah, mu rika la’antar su, don gudun ka da Ya karbi addu’ar mu Ya sa su zame mana masifa. Don kuwa Shi Ya zaba mana su. Allah Ya kiyaye. Daga Yakubu dahiru Gambarawa. 09038430566
Kira ga Katsinawa
Salam Edita daf atan kana cikin koshin lafiya amin. Don Allah ka isar da sakona ga Katsinawa akan korafe-korafen da suke yi akan wannan gwamnati mai albarka, karku manta Aminu Bello Masari yana kishin Jihar Katsina. Don Allah a kara hakuri. Daga Hon. Shamsu Muhammad Katsina. 07039878892
Mu rika dawo da ’yan majalisa
Assalamu alaikum Editan Aminiya Hausa ka ba ni dama in yi Allah wadai da matakan da wasu daga cikin Sanatocin Najeriya ke son dauka na hana shigo da kayan abinci cikin kasa, musamman ma Shinkafa bayan da gwamnatin talakawa ta Shugaba Muhammadu Buhari, ta amince da a shigo da abinci domun a samu saukin rayuwa a cigaba da manufan wannan gwamnati na kawo sauki ga talakawan kasa abin bakin ciki da takaici ne. Sai ga wasu ’yan hana ruwa gudu daga cikin Sanatocin mu na neman yin kafar angulu ga gwamnati da ma talakawan kansu Allah muna rokonka da ka yi mana maganin dukkan mai hannu wurin kuntata mana, ’yan Najeriya masu zabe cewa lokaci ya yi da mu za mu rika daukar matakin dawo da duk dan majalisar da zai kawo mana matsala a rayuwar mu. Daga Ahmadu Manager Bauchi 08065189242
Kira ga Gwamnatin Kebbi
Edita. Don Allah ka ba ni dama in isar da sakona a madadin al’ummar karamar Hukumar Jega.
Maiyama da Koko da Yawuri, cewa don Allah gwamnatin jiha da ta tarayya su taimaka su gyara mana hanyar babban titi, wadda ta tashi daga Jega zuwa Yawuri. Don wallahi hanyar nan ta yi mummunan lalacewa, hasali ma kusan kullum sai an samu matsalar ababen hawa da kan janyo asarar rayukka. A taimaka a gyara mana wannan hanyar don ceto rayukkan jama’a da ke salwanta sakamakon lalacewar hanyar. Daga karshe ina kira ga direbobi don Allah ku rage gudu yayin da suke kan aikin su, musamman kan wannan hanyar don tsira da rayuwar su. Daga Nasiru Musa Maiyama, Shugaban Muryar Talakawa, karamar Hukumar Maiyama, Jihar Kebbi [email protected]
Ga Wakilin Giwa da Birnin-Gwari
Edita al’ummar karamar Hukumar Birnin/ Gwari da Giwa da ke Jihar Kaduna mun yi sa’ar Jagoran da ke wakiltar mu a Majalisar Wakilai a Abuja.Tabbas! Kasancewar Alhaji Hassan Adamu Shekarau Jarman Birnin/Gwari dan majalisar Wakilai babbar nasara ce ga al’ummar Giwa da Birnin/Gwari, musamman idan aka yi la’akari da kyawawan halayen Jarman nan Birnin/Gwari, wadanda ke nuni da kishin yankinsa da son cigaban al’ummarsa baki daya idon aka dubi yadda ya rike shugabancin karamar Hukumar Birnin/Gwari a wasu shekarun da suka gabata. Daga Haruna Muhammad Katsina.Shugaban kungiyar Muryar Jama’a.07039205659 ko 07057491050