A lokacin da ni FDK na kishingida a karagarata, ina kallon yadda iska ke kada furanni a lambuna, a lokaci guda kuma ina karanto dimbin sakonnin da ma’abuta bibiyar shafin nan suka aiko mini:
Sakon farko daga Nasiru Kainuwa Hadeja (08100229688), wanda ke cewa: “Yi wa aboki kwacen budurwa ko yi wa kawa kwacen saurayi kai-tsaye ba za mu kira wannan al’amari da cin amana ba, domin wadansu suke yi wa masoyansu rikon sakainar kashi, sai sun kufce musu, su rika fadin an ci amanarsu.”
Daga Amirah K.A.U Kano: “Amincin Allah tare da kiyayewarSa su tabbata ga wannan Dasauyi, Allah Ya kara hada ka da basira, Allah Ya taimake ka FDK.”
Daga Tajudeen Kauran Namoda: “FDK, barka da kokari. Wannan labari na Dausayin Kauna yana nishadantar da mu masu karatun Aminiya.”
Sai kuma sakon Amina Sabi’u Waziri Bauchi, tana cewa: “FDK, ina yi muku fatan alheri, Allah Ya saka da alheri a kan wannan labarin na Farida da Alhaji Baba. Kuma ina tare da ku a kowane mako.”
Sai kuma sakon Umar Auwalu Naira (09037481184): “FDK, Ina mai maka fatan alheri. A gaskiya ni kan na fi maida hakalina ga Labarin Farida. Allah Ya taimaka, amin. Allah Ya ba da ikon kammala wannan kayataccen labari. Muna masu sauraranku a kullum, a koyaushe. Na gode.”
Daga Babawo Baras Funtuwa (08031810427), yana cewa: “Fatan alheri tare da kai FDK, Allah Ya kara basira da lafiya, amin.”
Ita kuwa Farida Idris daga Maiduguri a Jihar Barno (07082056873), cewa take: “Assalamu alaikum. FDK, Allah Ya kara ba ka damar karasa mana labarin Farida kuma Allah Ya kara daukaka jaridar Aminiya, na gode.”
Sako daga Murtala Aliyu: “Assalamu alaikum FDK, barka da dawoma wannan shiri namu mai albarka da fatar kana lafiya da dukkan mabiya wannan shiri; fatar alheri.”
Daga Dahiru Sunusi Mangal Kano, mazaunin birnin Abuja (08039500115), ya aiko dogon sakon da ke cewa: “Hajiya Farida, shure-shure fa ba ya hana mutuwa, idan namiji ya yi niyyar kara aure, duk duniya ba mai iya hana shi, domin kara aure fa dabi’ar da namiji ce. Jin dadi yana sa ya kara, domin ya kara samun jin dadin da ya fi haka. Haka kuma rashin jin dadi yana sa ya kara domin ya samu jin dadi. Don haka mata sai dai ku yi hakuri, komai daga Allah daidai ne. Don Allah ina son a gaida mini da mamata, Hajiya Halima Haruna Gwangwan da babana, Alhaji Sunusi Gwangwan da budurwata, rabin raina, Sahaibe Usman Gwangwan.”
Sa kuma sakon Binta Sani Bakori, da take cewa: “Labarin Jidalin Kishiya ya dauki hankali, ya kuma burge ni sosai. Ina fatar alheri, Allah Ya kara basira.”