Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta ce, Jihar Sakkwato ita ce kan gaba wajen yawan masu fama da talauci a Najeriya.
Rahoton binciken da hukumar da wasu hukumomi suka gudanar ya nuna ’yan Najeriya miliyan 133 — kashi 63 cikin 100 na al’ummar kasar — ke fama da talauci.
Binciken ya nuna mutum miliyan 86 daga cikin masu fama da talauci a kasar a Arewa suke, miliyan 47 kuma a Kudanci suke.
Alkaluman sun nuna a yayin da Jihar Sakkwato ke kan gaba da kashi 91 cikin 100 na matalauta, Jihar Ondo ce mai mafi karancin masu fama da talauci da kashi 27.
Gwamnatin Tarayya ta fitar da alkaluma ne bisa la’akari da fannoni lafiya da ingancin rayuwa da tsaro da rashin aiki da kuma fannin ilimi.
Ta sanar da alkaluman ne a wajen taron kaddamar shirin bincike kan talauci na kasa (MPI) ranar Alhamis a Abuja.
Binciken wanda aka gudanar tsakanin watan Nuwamba, 2021 zuwa Fabrairu 2022, ya tattaro alkaluma ne daga gidaje 56,000 da aka zabo a jihohi 36 na kasar, da kuma Abuja.