✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sai ranar 18 ga Janairu za a bude manyan makarantu

Gwamnatin Filato ta ce za ta bude makaratun gaba da sakandare a Jihar ranar 18 ga Janairun 2021, sabanin ranar da aka sanar da farko.…

Gwamnatin Filato ta ce za ta bude makaratun gaba da sakandare a Jihar ranar 18 ga Janairun 2021, sabanin ranar da aka sanar da farko.

Kwamishinan Ilimin Gaba da Sakandare na Jihar, Kakmena Audu ne ya sanar da hakan a ranar Asabar.

Da farko dai gwamnatin jihar ta sanya ranar Litinin 4 ga watan Janairu ne matsayin ranar dawowar makarantun domin ci gaba da darussa.

Kwamishinan ya ce Gwamnatin Jihar ta sauya ranar ce domin biyayya ga umarnin Kwamitin da Shugaban Kasa ya kafa domin yaki da COVID-19.

Mista Audu ya kuma umarnci daukacin shugabannin manyan makarantun da ke jihar da su tabbatar da bin umarnin tare da kiyaye matakan kariyar cutar COVID-19.