✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sai kowa ya taimaka wajen yaki da sauyin yanayi – FOMWAN

Gidajen Yada Labarai da kuma kungiyoyin Addini suna da muhimmiyar rawar da za su iya takawa wajen kawo karshen matsalar sauyin yanayi, kamar yadda aka…

Gidajen Yada Labarai da kuma kungiyoyin Addini suna da muhimmiyar rawar da za su iya takawa wajen kawo karshen matsalar sauyin yanayi, kamar yadda aka bayyana lokacin taron da kungiyar Islamic Green Club and Empowernment Initiatibes tare da hadin gwiwar kungiyar Mata Musulmi ta kasa (FOMWAN) suka gudanar a Abuja ranar Asabar da ta gabata.
daya daga cikin shugabannin kungiyar, Risikatu Bola Usman ta ce sun shirya taron ne saboda “nuna wa mutane muhimmancin shuka itace a muhalli, inda ta bayyana hakan da “sadakatul jariya.”
“Na fahimci cewa mutane ba su san aibun rashin yin hakan ba, a sakamakon haka ne nake kira ga shugabannin addini da gwamnati da su tashi tsaye wajen kawo sauyi wajen kare muhalli daga tabarbarewa,” inji ta.
A cikin wadanda suka halarci taron har da tsohon Daraktan Gidajen Rediyon Gwamnatin Tarayya wato (FRCN) Dokta S. A. Shu’aibu, inda ya yi kira ga ’yan jarida da su mayar da ido da hankalinsu wajen ilmantar da jama’a kan muhimmancin shuke-shuke a mahalli, ya ce: “Kodayake, abin mamaki yanzu shi ne irin yadda gidajen watsa labarai suka yi sake da irin wadannan muhimman abubuwa don neman kudi wajen harkokin ’yan siyasa wanda a wasu lokuta yin haka ya saba wa dokar aikin jarida,” inji shi.
Shugaban FOMWAN Hajiya Maryam Usman, ta ce gwamnati ta tashi wajen cimma wannan gagarumin aikin gyara muhalli sannan kuma kowa ya ba da  gudummawarsa., yan FOMWAN sunyi alkawarin bin Abuja da shuka itace.
A nata bangaren Hajiya Saudatu Mahdi WRAPA ta ce: “ana neman canji a komai, kamar yadda jam’iyyun siyasa suka samu sauyi, saboda haka gwamnati ta hana ciren itace ba tare da kwakwaran hujja ba, sannan kuma a nemi sauyin yawan amfani da itace wajen yin abinci don mafi yawan matan da ke kamuwa da ciwon zuciya, hayaki ke jawo hakan, dole mata su hada kansu wajen kare hakkinsu,” inji ta.