A ranar Juma’ar da ta gabata ce Sashen Hausa na Gidan Rediyon BBC, ya fitar da sakamakon gasar rubutun ‘Hikayata’ ta bana, inda labarin Safiyyah Jibril Abubakar ya yi zarra a cikin labarai kusan 300 da aka shigar gasar da su.
Alkalan Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta BBC Hausa, wato Hikayata, sun bayyana labarin ’Ya Mace a matsayin labarin da ya yi zarra cikin labaran.
Safiyya Abubakar Jibril, wadda malamar makarantar sakandare mai shekara 29 ce ta lashe gasar ta bana da labarinta mai suna ’Ya Mace.
Da take bayyana yadda ta ji bayan ta samu labarin nasarar da ta yi, marubuciyar ta ce, “Lokacin da aka kira ni a waya aka shaida mini cewa labarina ya yi nasara, sai na rasa me ma zan ce. Sai da na sake duba wayata don in tabbatar ba mafarki nake yi ba, da gaske kirana aka yi aka shaida mini cewa na yi nasara.”
Labarin ’Ya Mace a takaice na wata budurwa ce mai suna Halima, wadda ta shiga tasku bayan ta kai shekara 17 ba ta yi aure ba kuma babu wani tsayayye, alhali a bisa al’adar gidansu da yarinya ta kai shekara 14 ake aurar da ita.
Matsin lambar da take fuskanta daga iyayenta da sauran dangi ya sa ta amince ta auri wani mutum mai suna Garba, duk da cewa ba a gudanar da wani bincike a kansa ba. Ga shi kuma mahaifinta ya ja mata kunne cewa kada ta kuskura ta yarda a sake ta, domin idan ta dawo gida ba ya da halin daukar nauyinta.
Sanin hakan ya sa Garba yi wa Halima wulakanci iri-iri, har lamarin ya kai ga duka da zagi. A karshe dai auren ya mutu; da ta koma gida mahaifinta ya kore ta bayan ya lakada mata duka, sannan ya sha alwashin tsine wa duk wanda ya ba ta masauki a cikin ’yan uwansa.
Wannan ya sa Halima ta yanke shawarar tsayawa da kafafunta ta hanyar kama hayar daki a cikin gari da yin ayyukan hannu don ciyar da kanta. Sai dai ba a jima ba mai gidan ya samu labarin cewa ba ta da miji, ya ba ta notis cewa bai kamata mace irinta ta zauna a tsakanin mutanen kwarai ba.
Da suke bayyana dalilin zaben labarin ’Ya Mace a matsayin wanda ya yi zarra, alkalan gasar sun ce, wannan labarin ya ciri tuta ne saboda ya yi nauyi a galibin ma’aunan da aka yi amfani da su don tantance labarai 25 din da suka duba.
“Labarin ya tabo wata matsala da ke faruwa a wannan zamani, inda iyaye ke alla-alla su aurar da ’ya’yansu mata. Tunda aka fara labarin ake hawa, ake tashin hankali da jan hankalin mai karatu,” inji Bilkisu Yusuf Ali, daya daga cikin alkalan.
Jagoran alkalan, Farfesa Ibrahim Malumfashi ya kara da cewa, “Matsalar labarin da ya ce kawai, tun daga farko har karshe ake hawa, ba sauka. To amma shi ma wata dabara ce ta marubuta.”
Taurarin gasar ta bana su ne: Safiyyah Jibril Abubakar malamar makaranatar sakandare kuma daliba mai karatun digiri na biyu a fannin Kimiyyar kasar Noma a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, ta yi makarantar firamare a Zariya, sannan ta yi karatun gaba da firamare a garin Gwandu, Jihar Kebbi. An fi saninta da suna Safiyyah Ummu Abdoul a duniyar marubuta. Labarinta, ’Ya Mace shi ne ya zo na daya a gasar Hikayata ta 2018.
Wacce ta zo ta biyu, ita ce Sakina Lawal. An haife ta ce a Kaduna, inda ta yi karatunta na firamare da sakandare. Tana da takardar shaidar digiri a fannin Harshen Hausa, wadda ta samu daga Jami’ar Jihar Kaduna. Ita ce marubuciyar labarin Sunanmu daya wanda ya zo na biyu a gasar ta Hikayata.
Labarin Sunanmu daya shi ma labarin wata budurwa ne wadda kyanta ya rude ta har take ganin duk yadda ta ga dama za ta yi da maza. Da ta samu wani wanda take ganin ya dace ta aura shi kuma yana da mata, sai ta sa ya saki matar, amma bayan ta aure shi sai ta ga ashe dai kallon kitse ta yi wa rogo, don haka ta fita.
Daga bisani ta sake samun wani mai matar, amma suna son juna tsakani da Allah. Sai dai kuma bayan ta aure shi sai ta tarar ba wata ba ce matar illa wacce ta sa mijinta na farko ya saki.
Ita kuwa wacce ta zo ta uku a gasar, Bilkisu Muhammad Abubakar, a Kano aka haife ta. Yanzu haka daliba ce a Jami’ar Bayero ta Kano, inda take karatun Shari’a. Labarin da ta rubuta wanda ya kai ta wannan matsayi shi ne Zaina.
Labarinta mai suna Zaina shi kuma labari ne na wata mata mai suna Zaina, wacce mijinta ya yi batan-dabo bayan tashin bam. Bayan ta shekara shida tana jiran tsammani, sai iyayen mijinta suka matsa mata lamba a kan ta sake aure.
A karshe dai ta ba da kai ba don tana so ba, ta auri abokin mijin. Wata rana suna zaune sai ga mijin ya dawo ba zato ba tsammani.
Wannan gasa ta Hikayata wacce Sashen Hausa na BBC ya kirkiro, bana shekararta uku da farawa. Kuma kamar yadda hukumomin gidan rediyon suka bayyana, sun kirkiro ta ce da nufin bai wa mata damar fadin albarkacin bakinsu.
A gasar ta bana, baya ga labaran da suka yi na daya da na biyu da na uku, alkalan gasar sun kuma zabi wasu da suka cancanci yabo guda goma sha biyu, kamar haka:
Aurena 12
Kururuwar Ibilis
Lauren Tirmi
Nadama
Da kyar Na Sha
Bakar Rana
Kulu
Matallafina
Nakasa
Rubutaccen Al’amari
kalubale
Da Na Sani.
Alkalan gasar sun yaba da ingancin labaran da suka duba.