✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sadio Mane ba zai buga Gasar Kofin Duniya ba

Akwai bukatar a yi wa tauraron dan wasan tiyata a gwiwa.

Tawagar kwallon kafa ta Senegal ta bayar da tabbacin cewa dan wasan gabanta, Sadio Mane ba zai buga mata ko wasa daya ba a Gasar Kofin Duniya ta bana da za a yi a Qatar.

Senegal ta tabbatar da hakan ne a Yammacin ranar Alhamis, inda ta ce dan wasan bai murmure daga raunin da ya ji a gwiwarsa.

A ranar Talata ce Hukumar Kwallon Senegal ta bayyana cewa Mane mai shekara 30 ba zai buga wasannin farko na gasar ba bayan ta saka sunansa a jerin ’yan wasanta duk da raunin da ya ji.

Sai dai hoton gwiwar da aka dauka a ranar Alhamis ya nuna cewa akwai bukatar a yi wa tauraron dan wasan tiyata.

Mane ya fita daga wasan da kungiyarsa ta Bayern Munich ke fafatawa da Werder Bremen a ranar 8 ga watan Nuwamba sakamakon raunin.

Dama dai Bayern Munich ta bayar da tabbacin cewa Mane ba zai murmure a kan lokaci har ya samu damar wakiltar ba.

Wannan lamari ya jefa tawagar ta Senegal cikin damuwa kan raunin da kyaftin din nata ya ji, amma duk da haka ta sanya sunansa cikin jerin ‘yan wasan da za ta je da su wakilci a Babbar Gasar Tamaular da Qatar za ta karbi bakunci.

Da farko dai Hukumar Kwallon ta Senegal ta ce za ta yi duk mai yiwuwa ta hanyar amfani da malaman tsubbu don nema masa magani, amma bukata ba ta biya, wanda daga karshe kasar ta dauki dangana.