Sadaukin Sakkwato Malam Lawal Maidoki da mai alfarma Sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar II ya nada a ranar jumu’ar 12 ga Afrilu 2019 data gabata a gaban dimbin masoya, almajirai da masu yi masa fatan alheri.
Bayan kammala nadin Sarkin Musulmi ya yi jawabi ga mahalarta bukin domin su san dalilinsa na yin wannan sabon nadin, irinsa na farko a fadar mai martaba, abin da wasu ke ganin sarautar a matsayin kirkirarrar sarauta da ba ta da wani tushe wanda an yi haka ne don a faranta rayuwar wanda aka baiwa.
“Wannan sarauta da muka yi a yau ta Sadaukin Sakkwato ita ce ta farko a fadar Sarkin musulmi a kwaita cikin tarihi a baya duk masanin tarihi da daular Usmaniya yasan da haka.
“Sarauta ce, da ake baiwa mutum haziki jajirtacce mai rikon amana da yi wa addininsa aiki gwargwadon halinsa, da ni da duk wani wanda ya san Malam Lawal ya tabbatar da yana da wadannan halayen Allah ya karfafe shi da son addininsa da yi masa hidima, dubi yadda ya karfafa hukumar Zakkah da Wakafi ta jihar Sakkwato ya reneta tun tana kwamiti bayan rasuwar shugabanta na farko Farfesa Abubakar Gwandu. Yanzu hukumar ta shiga cikin jerin hukumomin zakka da wakafi na Duniya, abin da zai fi baka sha’awa ga kokarinsa yadda ya yi tsayin daka aka fahimci aikinsu da suke a Sakkwato baya da bambanci dana kasashen duniya aka bashi amana kuma ga ta nan ya rike” a cewar Sarkin Musulmi.
Haka ma ya kara da cewa, Sabon Sadaukin Sakkwato cikinsu yake, a shekara 12 da suka wuce yake aiki da shi bai taba ganin halin tir ko zamba a tare da shi ba, Malami ne mai son Allah da addini duk abin da zai yi yana sanya tsoron Allah ciki baya da kwadayi a harkokin zamantakewarsa ‘kan haka muka ga yakamata mu karrama shi da wannan sarauta don ya sanya wasu malamai kamarsa su san muna sane da duk wani mutum mai aikin addini don Allah, ba don wani kwadayi ba, za mu karrama shi, akwai Sadauki a jihar Kebbi an baiwa shugaba Buhari sarautar Sadauki mu ko anan Sakkwato mun nada Malam Muhammad Lawal Maidoki’ a cewar mai alfarma sarkin Musulmi.
Bayan kammala nadin an gudanar da babban taro na kungiyar Da’awa ta kasa na shekarar 2019 a fadar Sarkin musulmi wanda hakan karramawa ce da aka yi wa Sadaukin Sakkwaton a matsayinsa na daya daga cikin shugabanninta .
Sarkin Musulmi a wurin taron ya nuna damuwarsa ainun yadda bambancin siyasa ya raba kan mutanen kasar nan.
Ya ce, “In dai har Najeriya za ta tsinci kanta cikin wannan matsalar a 2019 ina tsoron abin da ke iya zuwa a 2023, ka ga ‘yan uwa sun daina magana, abokai sun rabu cikin fushi ana zage-zagen juna kafin zabe, makwabta na kin juna saboda kowanensu yana da jam’iyar siyasar da yake yi”
“Mu shugabannin addini a tsakiya muke ba mu da wani dan takara da muke goyawa baya. Yakamata mu kiyaye abin da za mu gayawa mabiyanmu mafiyawansu ba su da ilmi suna daukar duk abin da shugaba ya fadi gaskiya ne.
“Na bibiyi harkar zabe shekaru da dama ban taba fitowa fili da fili na goyi bayan wani dan takara ba, amatsayina na shugaban addini ban taba rokon limamai ko masu wa’azi su soki wani ba.” A cewar Sarkin Musulmi.
Ya Kuma ce, “Mu tambayi kanmu me yasa abubuwa suka canja ne ko saboda wasu shugabannin addini sun zama makwadaita ne suna karbar kudi su yi wa’azin goyon bayan wani dan takara? Bai dace a karfafa su ba don addini ya nuna a rungumi kowa a tafi tare”.
Sarkin Musulmi ya fahimci zaben 2019 ya kare a lokacin ne da yakamata a fara shirin na 2023.
“Yakamata mu fara shirin yadda za a samu zaman lafiya da fahimtar juna kafin da kuma bayan babban zaben kasa. Mu yi aikin samun zaman lafiya al’umma su zauna lafiya kowa ya yi zamansa inda yake so, mu hadu wuri daya don tun karar kalubalen da suka hana mana bin daidai.” In ji Muhammad Sa’ad.
Ya roki shugabannin addinai su yi kira kan zaman lafiya a kowane lokaci.
“Muna da kalubale a gabanmu wanda ba wanda zai musanya shi, don mun ji mun gani. Kana ganin matsalar tsaro da ta addabi Arewa maso Yamma.”
Sadaukin Sakkwato Muhammad Lawal Maidoki a kalamansa bayan kammala karatun Kur’ani na taya shi murnar Sarautar da Sarkin Musulmi ya ba shi ta Sadaukin daular Usmaniya ya ce, ya yi farinciki da godiyar Allah kan tarbiyatar da rayuwarsa ga son musulunci da yi masa hidima wannan yin Allah ne
“A koyaushe in aiki addini ya taso al’umma suka hadu wuri guda su aiwatar da shi sai naga bani kadai ne aka yi wa ba mu ne gaba daya don za mu hadu a tarayyar lada.
“Abin da muka al’adanta a kasar nan in aka yi nadin Sarauta a yi kade-kade da wake-wake da tabanjamanci kala-kala da suka sabawa karantarwar Dan Fodiyo, bayan kuma da shi ne muke koyi da kokarin martaba gidansa da kare abin da ya bari amma tashin farko ka saba ka mayar da sarauta ta gargajiya bayan hasken addini ya bayyana gare ka, Allah ya yi maka ni’ima sai ka saba masa hakan bai dace ba” a cewar Sadaukin Sakkwato.
Ya ce, ya ga ya dace da ya samu wannan ni’ima ya hada mutane a yi karatun kur’ani a roki Allah gafarar kuskuren da aka yi a baya cikin hidimar, ta haka za su saurari korafi ko gyara kan abin da suka yi su ‘yan Adam ne suna kasawa a bangarorin rayuwa daban-daban.
“Ina godiya da jinjina ga wadanda suka dauramin nauyin fatarsu ce gare ni suke zaton ina iya wa Allah ya bani kwarin guiwa. Da ba mu kusa ga masarauta muna ganin ana abin da bai dace ba, yanzu muna kusa za mu yi iya yinmu don ci gaban addini da musulmai, lokaci ya zo da ake bukatar hadin kan musulmi ganin yanda kuraye ke kokarin cinye mu, akwai bukatar rike martabar addininmu.
“Mutanen Sakkwato suna da martaba a idon duniya su rike martabar, a rika tuntubar jagororin addini a dukkan matsala ganin yanda Allah ya arzirta mu da Sarkin Musulmi mai saukin kai da daukar shawara da son ci gaban Musulunci, akwai bukatar hada hannu da shi don kara farfado da martabar addini a Najeriya.” In ji Maidoki.
A wannan karni na 21 da kide-kide da masha’a suka cika duniya musamman a wuraren bukukuwan aure da sarautu, nadin Sadaukin Sakkwato ya zo wa mutanen Sakkwato da mamaki yadda aka saba ganin nadin sarauta da bukukuwan sharholiya da nuna kasaita, wannan ya sha bamban da sauran ba wani tabanjama ko fito na fito da shari’ar Musulunci, an gabatar da makala kan magabata da aka yi da taron da’awa na kasa da walima tare da karatun kur’ani, lalle an fara samun sauyi a nadin Sarauta tun da aka fara nada malamai, majalisar sarkin musulmi ta yi zurfin tunani fara shigo da malaman addini ana nada su sarauta sabanin ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da aka saba gani rike da irin wadannan sarautu.