✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sace ‘yan matan Dapchi da Chibok sakacin APC da PDP ne

Assalamu Alaikum Edita da fatan ma’aikatanku na lafiya. Don Allah ku ba ni dama domin in bayyana ra’ayina a kan sace ‘yan matan makarantar Sakandarin…

Assalamu Alaikum Edita da fatan ma’aikatanku na lafiya. Don Allah ku ba ni dama domin in bayyana ra’ayina a kan sace ‘yan matan makarantar Sakandarin Dapchi da ke Jihar Yobe A Najeriya. Hakika wannan abin takaici ne da Allah wadai, kuma ya nuna mana karara cewa Gwamnatin APC ta yi sakaci wajen sace ‘yan matan makarantar Dapchi, kamar yadda Gwamnatin PDP ta yi sakacin sace ‘yan matan Chibok a shekarun baya. Tabbas wannan ba karamin sakaci ne ba ga Gwamnatin APC. Kuma muna kira da babbar murya kawai su ceto wadannan ‘yan matan. Daga karshen nake kira ga masu zargin jam’iyyar mu ta PDP da shirya makarkashiya da sace ‘yan matan makarantar Dapchi. Domin shirya wa Gwamnatin Buhari makarkashiya, ta yadda za a bata mata suna. Wannan sam ba abin da ya dace ba ne kuke yi, domin mu da aka sace ‘yan matan Chibok ba mu zargi kowa ba. Don haka kawai hanya mafi sauki ga  Gwamnatin ‘yan canji ta Abuja da a kwato wa lyaye ‘ya’yansu da aka sace a makarantar Dapchi da ke Jihar Yobe daga karshe gwamnoni da sauran shugabanni masu karya, ku daina domin wannan karyar da aka yi a Jihar Yobe na kwato wadannan ‘yan matan sam bai dace da fatan Shugabannin APC za a saki karya a kama gaskiya.

Daga Comrade Arabiyyu Muhammad Gidan Madi A Jahar Skokto A Najeriya, 08067873852 [email protected]