Godiya da yabo da tsarkakewa sun tabbata ga Allah wanda Ya sanya dare da wuni su kasance ma’aunan gane lokuta. Kuma Ya sanya su domin gane kwanaki da shekaru da kuma lissafi.
Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halitta shugabanmu Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa wanda aiko shi ya zama salsalar fitar da mutane daga duffan zalunci da shirka da tabewa zuwa ga hasken adalci da imani da shiriya.
A yau Juma’a ce muka shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1409 Bayan Hijirar Annabi (SAW), kuma muna fata Allah Ya yi mana dandazon alheri a cikinta. Kuma Ya raba mu da sharri da bala’in da duk wata cutarwa da suke cikinta.
Bayan haka, hakika mafi yawan Musulmin Najeriya, suna gafala daga al’amarin sabuwar shekarar Musulunci, sun fi sanin watanni da kidayar shekarar Nasara wadanda ka gina su kan kalandar Gregory. Wannan ya sa da yawan Musulmi ba su ma sanin yaushe shekarar Musulunci ke shigowa ba, wani ma ba ya sanin kwanan watan Musulunci nawa ne sai lokacin azumi ko Sallah. Musulmi da dama a yau da za a tsare su a ce su lissafa watannin Musulunci sai dai su shiga kamekame, ba su san su ba, kuma ba su nufin su sani!
Amma babban abin bakin ciki da za ka tambaye su yau watan Nasara ko watan ’yan albashi nawa ne, suna iya kawo su da kwanakinsu cikin waka saboda tun a firamare an karantar da su hakan. Wato wakar nan ta‘Thirty days has September,’ da take rubuce a jikin wasu littattafan rubutu. Ganin wannan hali da muke ciki ne ya sa muka gabatar da wannan dan takaitaccen bincike kan shekara da watannin Musulunci. Muna fata zai taimaki Musulmi su fahimta tare da aiki da watanni da kidayar Musulunci.
Shekarar Musulunci tana farawa ce daga ranar 1 ga Muharram na kowace shekara, kuma kidayar Kalandar Musulunci ta dogara ne a kan ganin jinjirin wata ba a kan lissafin awoyi ko kwanaki bisa kitance ba. Shi kuma jinjirin wata yana iya kamawa a ranar 29 ga wata mai shudewa, in ba a gani ba a cika kwana 30, washegari ya zama 1 ga sabon wata.
kidayar watannin Musulunci ta samo asali ne daga ranar da Allah Ya halicci sama da kasa. Amma a samar da tsarin kidaya ta dindindin domin adana tarihi sai al’ummar Musulmi suka dora kidayar bisa mizanin Hijirar Ma’aiki (Sallahu Alaihi Wasallam) daga Makka zuwa Madina.
Shekarar Musulunci tana da wata 12, kuma yawan kwanakin watan ya dogara ne kan ganin jinjirin wata, ana ganin mafi yawan shekarar ba ta wuce kwana 354. Kuma kamar yadda muka fadi, shekarar takan fara ne da watan Muharram kuma ana jingina ta da Hijira, wannan ya nuna cewa da watan Muharram da shekarar Hijirar in an nazarce su za a ga cewa ba an jingina su ne ga wani mutum mai girma ko wani gunki ko tarihin haihuwa ko mutuwar wani mashahurin mutum ba, an jingina su ne ga wani muhimmin al’amari da ya shafi shi kansa addini da daukakarsa da juyin-juya halin da ya haifar a wancan zamani da zamunnan da suka biyo baya har zuwa tashin kiyama.
Watan Muharram da Hijira suna da gagarumar rawar takawa wajen sanin muhimman al’amurran addini. Don haka saninsu a tarihance da abubuwan da suka faru a cikinsu tare da nazartar darussan da suke kunshe a cikinsu na da muhimmanci ga kowane Musulmi.
Allah (SWT) Ya nuna cewa kidayar watanni a wurinSa guda goma sha biyu ne tun daga ranar da Ya halicci sammai da kasa. Sai dai sakamakon yadda duffan kafirci da shirka da al’adu ke lullube shiriya, ya sanya, kowace al’umma ta sanya wa wadannan watanni sunan da take ganin sun dace da ita.
Misali a nan kasar Hausa ana kiran Muharram da watan Cika-ciki, akwai watan Bawa da watan JuyaBai da sauransu. To haka ma lamarin yake ga Larabawa, inda suka sanya wa watanni sunaye dabandaban, kafin Allah Ya mayar da al’umma kan sunayen watanni na asali ta hanyar aiko da Shugaban Manzanni, Annabi Muhammad (SAW) kamar yadda za mu gani a nan gaba.
Muharram da sauran watanni a tarihance:
Watan Muharram shi ne mabudin Sabuwar Shekarar Musulunci, Shekarar Musulunci tana sanya sabuwar riga da zarar ya kama. Yana daya daga cikin watanni hudu masu alfarma a wurin Larabawa kafin zuwan Musulunci da kuma bayan zuwansa. Sauran watanni masu alfarma su ne Zul-kida da ZuI-Hajji da suke zuwa kafin Muharram din. Cikon na hudun shi ne watan Rajab wanda ke ware. Larabawa a zamanin Jahiliyya suna haramta wa kansu kai hari ko takalar yaki a cikin wadannan watanni.
Watannin Musulunci wadanda dukkansu suna dogara ne da kamawa da karewar wata a sararin samaniya su ne: Al-Muharram, Safar, Rabi’ul Awwal, Rabi’us Sani, Jimada Ula, Jimada Akhir, Rajab, Sha’aban Ramadan, Shawwal, Zul-kida da Zul-Hajji.
Sunayen watanni a wurin Larabawan Farko da Zamanin Jahiliyya
Wadansu ’yan kwakkwafi daga masana tarihi sun ce Larabawan farko-farko, (AI-Aribah) suna kiran watannin sama da sunaye kamar haka:
Muharram da Natikan ko Mu’utamar, Safar da Najir ko Annajaru, Rabi’ul AwwaI da Khawwan, sauran su ne: Sinwanu, Hanin ko Rubiy, Rayinu ko Ba’adah, Alasmu, Wa’aglu ko Wa’il, ko Adil, Nakik, ko Na’il, Wa’al, ko Waglun, Hawa ko Rannah, sai kuma Barkun cikon na goma sha biyu.
Sunayen watannin a yanzu kuma an ce sun samo asali ne a zamanin wani Kakan Annabi (SAW) mai suna Kullabu Bin Murrah wanda ya rasu shekara 200 kafin aiko Annabi (SAW). Sai dai Musulunci ya yi wa watanni ko mu ce sunayensu gyare-gyare tare da tsame su daga camfecamfe.
Kuma duk da cewa Larabawan Jahiliya na kiransu da sunayen da muka san su a yau, sai dai babu wata kwakkwarar madogara kan da wane wata suke fara kidayar shiga sabuwar shekara. Akwai dai bayanan da suke cewa mutanen Makka suna fara kidayar Sabuwar Shekara ce daga watan Muharram. To amma abin tambaya wane Muharram? Domin su Larabawan Jahiliya suna kiran watan da muke kira Muharram a yau da mai bi masa da sunan Safar ne. A lissafinsu akwai Safar na Farko da Safar na Biyu, maimakon Muharram da Safar, kamar dai yadda ake da Rabi’ul Awwal da Rabi’us Sani ko Jimada Ula da Jimada Akhir.
Dalilin kiransa da watan Muharram
Ya zo cikin littafin Nihayatul Arab, cewa dalilin da ya sa Larabawan Jahiliya suke kiran watan Muharram da wannan suna shi ne sun taba kai harin yaki a cikinsa suka sha kashi. Domin haka sai suka haramta wa kansu yin yaki a cikinsa. Kuma suka kira shi da watan Muharram, wato Mai alfarma wanda ba a tsokana ko yin yaki a cikinsa. A zamanin Jahiliyya jeranta watanni masu alfarma na da matukar wahala ga Larabawa saboda sabonsu da yake-yake da kai hare-hare, don tara dabbobi wadanda su ne
ginshikin tattalin arzikinsu ko domin daukar fansa game da jinin wani dan uwansu da wata kabila ta kashe. Domin haka sai suka bullo da wani tsari na jinkirtawa ga Muharram ta yadda zai zamo kamar babu wani wata mai alfarma face watannin Zul-kida da ZulHajji. Don haka sai su fara kidayar Sabuwar Shekara daga watan Safar.
Tarihi ya nuna cewa, wani mutum daga kabilar Bani Malik Bin Kinanah mai suna Huzaifa Bin Ubaidah da ake yi masa lakabi da Alkalamisiy, shi ya shahara da wannan jinkirtawa. Da ya mutu sai dansa Kali’u Bin Huzaifa ya gaje shi a kai. Kali’u ya riski Musulunci, sai dai Abu Tamama ne mutum na karshe da ya yada wannan al’ada ta jinkiri bayan da Musulunci ya yi hani a kansa.
Yadda Larabawa suke yin wannan jinkiri shi ne idan suka kammala aikin Hajjinsu sukan taru zuwa ga mai bayyana jinkirtarwar, sai ya mike a cikinsu ya ce, “Ni na halatta daya daga cikin watannin Safar din nan biyu, Safar din Farko, kuma na jinkirtar da daya Safar din sai shekara mai zuwa.”
Bayyanar Musulunci ke da wuya sai watanni masu alfarma suka koma kamar yadda suke a farkon halitta inda Allah Madaukakin Sarki Ya haramta wannan al’ada ta jinkirtawar cikin fadinSa: “Abin sani kawai jinkintarwar nan kari ne kawai a cikin kafirci.” Shi kuma Ma’aiki (SAW) cikin Hajjinsa na Ban-Kwana ya ce, “Ku saurara! Lallai zamani ya juyo kamar yadda Allah Ya tsara shi a ranar da Ya halicci sammai da kasa,” wato yana nufin cewa sunayen watanni sun komo kamar yadda suke a farkon halitta, kafin al’adu su shigo su jirkita su. Kuma ga shi an haramta amfani da al’adar nan ta jinkirta wani wata don ya fada wata shekara bayan tsawon zamani da aka share ana yi a matsayin abin da mutane suka yi imani da shi tare da mayar da shi addini kaka da kakanni.