Mutanen yankin Masarautar Dansadau a Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara sun firgita bayan ganin wata sabuwar kungiyar masu dauke da makamai da ake yi wa ’yan bindiga wa’azi su daina kai wa al’ummomi hari.
Ganau sau ce shaida wa wakilinmu cewa a ranar Juma’ar da ta gabata ce ’yan sabuwar kungiyar da ake zargin ta addini ce suka isa unguwar Dandalla a kan babura, amma ba su halarci sallar Juma’a tare da sauran jama’a ba; kebewa suka yi, suka yi tasu.
- An je kotu nema wa Buhari da gwamnoni wa’adi na uku
- Yadda Matsalar Shaye-Shaye Ta Zama Ruwan Dare A Najeriya
Majiyarmu a garin Dandalla ta ce bayan mutanen sun idar da sallar sai suka fara wa’azi suna kira ga ’yan bindiga da su daina kai wa al’ummomi hari.
A cewar masu wa’azin, maimakon kai wa manoma hari da hana su aiki a gonakinsu, gara ’yan bindiga su dauki makami su yaki jami’an gwamnati.
Garin Dandalla na da tazarar kilomita 15 da garin Dansadau, wanda ke kusa da dajin da ya ratsa har zuwa Birnin Gwari a Jihar Kaduna da ke makwabtaka da Jihar Zamfara.
Wazirin Dansadau, Alhaji Mustapha Umar, ya shaida wa Aminiya cewa wani mazaunin garin ya tabbatar masa da faruwar lamarin.
“Gaskiya ne mutanen da ke dauke da makamai sun shigo cikin garin, hakan kuma ya sanya fargaba a zukatan mutanen yankin da tunanin sabuwar kungiyar na da akida irin ta Boko Haram,” inji shi.
Alhaji Mustapha wanda a baya ’yan bindigar sun yi garkuwa da shi na tsawon makonni kafin su sako shi bayan an biya kudin fansa, ya ce a lokacin da aka yi garkuwa da shi wani dan bindiga ya harbe daya daga cikin ’yan kungiyar saboda ya yi musu wa’azi cewa su daina abin da suke yi.
“Kisan dan kungiyar ya haifar da kazamin fada a tsakaninsu da ’yan bindigar kuma kashe ’yan bindiga masu yawan gaske.
“Abin da na lura a lokacin da nake hannun ’yan bindigar shi ne su kansu sun firgita da ayyukan ’yan wannan kungiya mai dauke da makamai a cikin dajin,” inji shi.
Al’ummomi, musamman a yankunan Kudanci da Gabashi da ma Yamma garin Dansadau sun shafe shekaru suna ganin ta kansu a hannun ’yan bindiga.
Abin ya kai ga ’yan bindigar ne ke da iko a kan mazauna kuma su ne ke yin hukunci tsakanin mutane a duk lokacin da aka samu sabani.