Sabuwar hukumar nan mai yaki da yaduwar manya da kananan makamai ta kasa (NATCOM) ta ce ta kammala shirin daukar mutum 300,000 aiki a fadin Najeriya.
Hukumar ta ce za ta dauki mutanen ne sannan ta horar da su don dakile yaduwar makamai a daidai lokacin da ake fama da kalubalen tsaro.
- Nijar ta yanke wa ofishin jakadancin Faransa ruwa da wuta
- NAJERIYA A YAU: Yadda Buɗe Madatsar Lagdo A Kamaru Zai Shafi ’Yan Najeriya
Mai rikon mukamin shugaban hukumar, Otunba Adejare Rewane ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Lahadi.
Ya ce hukumar za ta dauki mutum 7,000 aiki a kowacce Jiha ta Najeriya da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
A cewarsa, “Za mu debi mutum 300,000 aiki a fadin Najeriya domin kasarmu ta zauna lafiya.
“Ba kawai daukarsu aiki za mu yi ba, za a ba su isasshen horo. Hakan kuma zai taimaka wajen rage matsalar rashin aikin yi a kasa. Za mu hada kai da sauran jami’an tsaro don ganin mun sami nasara.
“Game da daukar mutum 7,000 da za mu dauka, masu son a dauke su sai su rika duba jaridu domin ganin bayanai da ka’idoji. Amma dai za mu fi ba matasa masu jini a jika fifiko wajen daukar aikin,” in ji shugaban.