✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabon Shugaban Nijar ya sha rantsuwar kama aiki

An rantsar da Bazoum kwana biyu bayan sojoji sun yi yunkurin juyin mulki

Sabon Shugaban Kasar Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum ya sha rantsuwar kama aiki, kwana biyu bayan wasu sojojin kasar sun yi yunkurin hambarar da gwamnanti.

Bazoum ya zama Shugaban Jamhuriyar Nijar na 11 bayan ya karbi rantsuwar dauke da Al-Kur’ani a gaban Kotun Tsarin Mulkin Kasar a ranar Juma’a.

A jawabinsa bayan karbar ranstuwa, Bazoum ya ce gwamantinta za ta gudanar a mulki bisa bin tanade-tanaden tsarin mulkin kasar ta yadda ba za a samu tarzoma irin wadanda aka samu a baya ta dalilin wasu matsaloli ba.

Shugaban Kotun Kolin kasar, Mai shari’a Bouba Mahaman ne ya rantsar da Bazoum, zababben shugaban kasar an farko da ya karbi mulki daga zababbenen shugaba bisa tsarin dimokuradiyya a tarihin kasar.

An gudanar da bikin rantsuwar ne bisa tsauraran matakan tsaro, kuma ya samu halarcin shugabannin kasashe da na diflomasiyya daga ciki  da wajen kasar, baya ga wasu manyan baki daga wurare daban-daban.

Bazoum mai shekara 60, shi ne tsohon Ministan Harkokin Cikin Gidan kasar, kuma na hannun daman Shugaba Mahamadou Issoufou mai barin gado.

Ya lashe zaben da aka gudanar a watan Fabrairu da kashi 55.7 inda ya kayar da babban abokin karawarsa kuma tsohon Shugaban Kasar, Mahamane Ousmane.

Aikin da ke gaban Bazoum

Bazoum na da babban kalubale a gabansa na jagorantar kasa mafi talauci a duniya, inda kashi 40% na ’yan kasar ke fama da fatara.

A baya ’yan kasar sun gudanar a zanga-zangar neman sauye-sauyen tattalin arziki.

Akwai kuma matsalar kungiyoyin tayar da kayar baya da suka addabi kasar.

A cikin wata uku na farkon 2021, ’yan bindiga sun kashe fiye da mutum 300 da suka hada da sojoji da farar hula da ke addabar kasar.

Kasar ta sha fama da juyin mulki a lokuta daban-daban, na karshe shi ne wanda aka yi wa gwamnatin Mahamadou Tandja a 2010, sai kuma wanda aka dakile a ranar 31 ga watan Fabrairu, 2021.

Ana jiran ganin kamun ludayinsa, musamman ganin yadda ya yi alkawaron dorawa a kan ayyukan uban gidansa, Mahamadou Issoufou wajen yaki tabbatar da tsaro da farfado da tattalin arzikin kasar.

Kafin saukar Issoufou, ya samu lashe kyauta a matsayin Shugaban Afirka wanda ya fi iya gudanr da mulki, saboda kokarinsa wajen inganta tattalin arzikin kasar da sauransu.