Wani sabon rikici tare da asarar rai ya barke tsakanin al’ummar Hausawa da Yarabawa a garin Ibadan, Jihar Oyo.
Mazauna Unguwar Mobil a kan babbar hanyar MKO Abiola a birnin Ibadan sun shafe yinin Lahadi cikin halin dar-dar a sakamakon kaurewar fada tsakanin Yarbawa da Hausawa masu sana’ar acaba.
- Binciken kwakwaf: Su wane ne ’yan bindigar da suka addabi Zamfara?
- Layin karbar abincin Mariya: Taimako ko kashe zuciya?
Mutum daya ya rasa ransa kafin isowar jami’an tsaro da suka kwantar da rikicin daga baya.
Aminiya ta jiyo daga majiya mai tushe cewa rikicin ya faro ne daga wata rashin jituwa tsakanin wani mai shago da abokin cinikinsa a inda wani dattijo mai suna Mufutau Sanni da ake yi masa lakani da Baba-Ijebu ya shiga tsakani domin sulhuntawa.
Sai dai majiyar ta ce bangare daya na masu jayayyar, mafi yawancinsu ’yan Arewa ne masu sana’ar acaba, ba su ji dadin sasantawar da Baba-Ijebu ya yi ba, a inda suka far masa da duka da yayi sanadin samun raunuka a jikinsa.
An garzaya da Baba-Ijebu zuwa wani asibiti da aka tabbatar da mutuwarsa, inji majiyar da ta kara da cewa, “Wannan ne dalilin da ya harzuka matasan Yarbawa suka yi yunkurin daukar fansa da ya haifar da barkewar fada a tsakanin wadannan al’ummomi biyu mazauna Unguwar Mobil.”
Rundunar hadin guiwa ta ’yan sanda da jami’an tsaron Amotekun sun hanzarta isa wannan wuri da suka shawo kan lamarin kafin ya kazanta.
Sai dai a lokacin da Aminiya ta tuntubi Sarkin Hausawan Mobil, Malam Sulaiman Mati Garba, ya ce “A gaskiya lamarin ya auku ne a lokacin da na yi nisa da wannan wuri.
“Wani amini na bayarabe (da aka sakaya sunansa) da ya bugo min waya ya ba ni shawarar kada in kuskura in kusanci wannan wuri.
“Amma bayanan da na samu sun nuna cewa wadannan fusatattun Yarbawa sun samu damar yin amfani da jami’an tsaro wajen farfasa rumfuna da shaguna mallakar Hausawa da suka yi awon gaba da dukkan muhimman kayan wayoyi da babura da sauransu.”
Da yake tofa albarkacin bakinsa, wani bahaushe mazaunin Ibadan, Alhaji Hayatu Ibrahim ya dora laifin aukuwar irin wannan fada tsakanin Yarbawa da Hausawa a kan rashin hakurin Hausawa inda ya ce, “Muddin Majalisar Sarkin Hausawan Ibadan ta kasa daukar matakin nada shugabannin ’yan Arewa masu sana’ar Okada a sassa daban-daban na birnin Ibadan, to kuwa Wallahi Tallahi za mu yi nadama a nan gaba domin mafi yawancin fadan da ake yi a tsakanin Yarbawa da Hausawa a Ibadan irin wadannan ’yan Okada ne suke janyo shi domin babu inda za ka samu shugabanni masu tsawatarwa a cikinsu.”
Har zuwa lokacin kammala rubuta wannan rahoto, Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Oyo ba ta yi bayani a hukumance dangane da wannan lamari ba.