✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sabon albashi: Za a fara biyan ma’aikatan Kananan Hukumomin Filato

Lalong ya ba da umarnin kammala shirye-shiryen biyan su cikin gaggawa

Gwamnatin Filato ta amince ta fara biya ma’aikatan Kananan Hukumomi a fadin jihar da sabon mafin karancin albashi na N30,000.

Hakan na zuwa ne bayan zanga-zangar da ma’aikatan kananan hukumomin jihar 17 suka gundanar na tsawon lokaci a garin Jos, suna neman a biya su da sabon albashin na N30,000.

Daga karshe dai a ranar Alhamis Gwamnatin Jihar ta amince fara biyan ma’aikatan kananan hukumomin, kamar yadda suka bukata.

Wata sanarwa da ke dauke da sanya hanun Babban Sakataren Hukumar Kananan Hukumomin Jihar, Henry K. Lankwap ce ta bayyana haka.

Sanarwar ta ci gaba da cewa Gwamnatin Jihar Filato, ta amince da hakan ne a taron gaggawa da ta yi a Gidan Gwamnatin Jihar.

Ya ce gwamnatin ta umarci Hukumar Ma’aikatan Kananan Hukumomin ta shirya dukkan wasu tsare-tsare na ganin an fara biyan ma’aikatan da sabon albashin batare da bata lokaci ba.