Ministan Sufuri, Rotomi Amaechi ya ce a boye ake sata a gwamnati mai ci ta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake amsa tambaya a wata tattaunawarsa da Daily Trust.
Da aka tambaye shi ya yi tsokaci a kan babban abin da za a iya tunawa da gwamnatin Buhari wacce yanzu take da kasa da watanni 21 kafin karewar wa’adinta, Amaechi ya ce gwamnatin ta APC ta tafiyar da gwamnati fiye da na baya.
A cewar ministan, sabanin a gwamnatocin baya da mutanen da ba a san hakikanin sana’o’insu ba suka zama attajirai dare daya ba tare da an hukunta su ba, hakan ba ya faruwa yanzu a mulkin Buhari.
“Ina so ’yan Najeriya su fadi gaskiya; zai yiwu mutum ya dibi kudi a zahiri a wannan gwamnatin? Ba ina cewa ba a sata ba ne.
“A dauka ma muna yi, za ka iya dibar kudi a bayyane a wannan gwamnatin? A baya ya ake yi? Za ka iya diba duk yadda ranka yake so. Rashawa ta yi katutun da ba a ma magana a kanta. Mutane ko kunyar bayyana abin da suka sata ba sa ji.
“Yawancin wadanda suka yi satar babu wani abin ku-zo-ku-gani da suke da shi a baya, ba su da ko shagon kafinta, amma sun zama attajirai, kuma ba sa ko jin kunyar boyewa. Amma yanzu ko za ka sata, sai dai ka yi a boye. Ba wai ina cewa yin hakan abu ne mai kyau ba.
“A baya za ka iya yin sata kuma babu wanda zai kama ka, in kuma an kama, to babu wani hukunci da zai biyo baya. Amma yanzu kuwa ta sauya zane,” inji Amaechi.