✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da Kwankwaso zai dawo APC — Ganduje

Haɗakar da wasu ‘yan siyasa ke ƙoƙarin yi domin ƙalubalantar Shugaba Tinubu a Zaɓen 2027 ba za ta yi tasiri ba.

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa ƙiris ya rage madugun jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya dawo jam’iyyarsu ta APC.

Gamduje ya bayyana hakan ne yana mai cewa jam’iyyar NNPP ta mutu murus, kuma jana’izarta kaɗai suke jira a gudanar a nan kusa.

Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin ziyarar da wata ƙungiya mai goyon bayan Shugaba Bola Tinubu (TSG) ta kai sakatariyar APC ta ƙasa da ke Abuja.

Ganduje ya ce APC a kodayaushe tana cikin shirin karɓar jiga-jigan ‘yan siyasa ciki har da Kwankwaso “idan har ya yanke shawarar dawowa gida.”

Ganduje ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP ta rasa duk wani karfi da tasiri da take da shi, musamman a Jihar Kano, inda ya ce ‘yan jam’iyyar da dama sun bar ta.

Ya ce: “NNPP ta mutu. Kuma ba da jimawa ba za a birne ta. Amma abin da ya rage shi ne a haƙa kabari, kuma har an fara hakan. Muna jiran a kammala shiri ne kawai.”

A cewarsa, “Kwankwason ya fara yunƙurin dawowa APC saboda ya fahimci cewa ya rasa komai a jam’iyyar da ya tallata.”

“Ƙofa a buɗe take ga duk wanda ya shirya dawowa APC”, yana mai cewa Kwankwaso zai samu tarba mai kyau idan ya dawo gida.

“Za mu karɓe shi idan ya dawo, domin gida zai dawo,” in ji Ganduje.

Ya ƙara da cewa APC ta na ci gaba da karɓar fitattun ‘yan siyasa daga sassa daban-daban, wanda hakan ke ƙara ƙarfafa jam’iyyar a faɗin ƙasar.

Haɗakar ’yan adawa ba za ta yi tasiri ba — Ganduje

Shugaban jam’iyyar ta APC ya kuma ce haɗakar da wasu ‘yan siyasa ke ƙoƙarin yi domin ƙalubalantar Shugaba Tinubu a Zaɓen 2027 ba za ta yi tasiri ba “domin kuwa rushewa za ta yi kafin a je ko’ina.”

Ganduje ya ce: “Wannan haɗakar da ake ta surutai a kai, za ta tarwatse kafin ta gama haɗuwa. Yawancin su za su dawo cikin APC, domin sun san cewa nan ne gida.”

Ganduje ya jaddada cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da jan ragamar mulki a Nijeriya saboda ingantattun manufofi da kuma salon shugabancin Tinubu.