✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ruwan Sama Ya Raba Mutane 1000 Da Gidajensu A Kogi

Zai yi wahalar gaske a samu wanda zai iya sake gina gidansa da kansa, muna roƙon a taimaka mana.

Mamakon ruwan sama ya yi sanadiyar rushewar  daruruwan gidaje a Jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya. 

Ruwan ya yi wannan ta’adi ne a ƙauyen Iyara da ke Karamar Hukumar Ijumu a ranar Litinin ɗin da ta gabata.

Bayanai sun ce hakan ya jefa mutane sama da dubu guda cikin mawuyacin hali na gudun hijira a waɗansu ƙauyukan.

Sarkin ƙauyen Iyara, Oba Jacob Meduteni ya bayyana alhini kan faruwar lamarin.

Ya kuma roƙi gwamnati da masu hannu da shuni da su taimaka wa waɗanda abin ya shafa.

Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar Iyara na kasa, Alhaji Aliyu Badaki ya ce sama da mutane dubu ne iftila’in ya shafa.

Ya ce, wannan iftila’in ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da matsanancin talauci da tsadar rayuwa a kasar nan.

Adebayo Bamisaiye wani da abin ya shafa ya roƙi a taimaka musu domin an jima ba a tsinci kai a cikin irin wannan yanayi ba.

Ya ce, “A halin da ake ciki a ƙasar nan na tsadar kayayyaki, zai yi wahalar gaske a samu wanda zai iya sake gina gidansa da kansa, muna roƙon a taimaka mana.”

Sama da mutane dubu ne ruwa ya raba da matsugunansu a kauyen Iyara da ke Jihar Kogi.