Wani yaro ya rasu a yayin da wasu suka jikkata a wajen kwasar ‘ganima’ a gine-ginen da Gwamnatin Jihar Kano ta yi rusau a Filin Idi.
Aminiya ta gano lamarin ya faru ne yayin da matasa suka yi wa wani gini kawanya domin kwasar dibar karafunan rodi da kofofi ne wata babbar mota ta take yaron.
- NAJERIYA A YAU – Shin Buhari Zai Iya Rayuwa A Daura?
- Muhimman abubuwa 10 da Gwamnan Kano ya aiwatar a kwana 10 na mulkinsa
Wani Ganau ya ce “Muna tsaye a nan lokacin da yaron da wasu suka fito da kwano na rufi da wasu kofofi da rodi.
“Ba mu san wa ya biyo su ba. Suna da yawa amma yaron da ya yi rashin sa’a yana fitowa wata tirela ta take shi kuma nan take ya rasu.”
An ruwaito cewar ana fargabar wani ma ya rasu yayin da suke tsaka da dibar ‘ganima’ gini ya rufta musu.
Kakakin ’yan sandan jihar, SP Haruna Abdullahi Kiyawa, ya ce sun cafke mutum 49 da ke satar dukiyar al’umma da sunan ganima, a irin wadannan gine-gine da aka rushe.
Ya ce: “Wasu daga cikin kayan da muka kawo sun hada manyan kofofi, taga, na’urar sanyaya wuri guda hudu, karfe rodi guda takwas da kuma manyan guduma guda 16.”