Rundunar sojojin Jamhuriyar Nijar ta ce wasu jerin hare-haren kwanton ɓaunar da aka kai ƙasar, ya yi sanadiyar mutuwar jami’anta 12 da raunata wasu 30.
A cewar rundunar, an kai hari na farko ne a yammacin Tillaberi a ranar Lahadin da ta gabata, inda aka kashe sojoji biyar da raunata wasu 25.
Rundunar ta kuma ce wasu jami’anta biyar da ke gudanar da aikin sintiri a yankin Diffa, da ke fuskantar hare-haren mayakan Boko Haram sun mutu, sanadiyar wata fashewa da aka samu.
Sai dai rundunar ta ce a martanin da ta maida a wasu hare-hare ta sama da kuma kasa, ta samu nasarar kashe ’yan ta’adda da dana da suka kai harin.
- Yadda ’yan uwanmu 18 suka mutu a hatsarin ’yan Maulidi
- Jerin tallafin ambaliya da ya shiga hannun Gwamnatin Borno
Haka nan a wasu hare-haren da ƴan tawayen MPLI sukai, sun kashe sojoji biyu a yankin Arewacin Agadez, sannan suka raunata wasu 6, duk da cewa runudar ta ce ta maida martani kan ’yan tawayen da ke kokarin tserewa zuwa iyakarta da Libya.
Tuni dai ƙungiyar ta MPLI wacce reshe ce a cikin ƙungiyar FPL ta yi iƙirarin kashe sojoji 14 da jami’an Jandarma biyu, sannan ita ma ta rasa mayakanta biyu a wannan hari da ta kai.
A cewar wasu alƙaluma, kimanin sojoji da fararen hula dubu daya da dari biyar ne suka rasa ransu a Nijar sanadiyar hare-haren masu iƙirarin jihadi a cikin sama da shekara daya, wanda hakan ke nuna yadda aka samu ƙaruwar asarar rayukan daga dari 650 da aka samu daga watan Yulin shekarar 2022 zuwa na 2023, lokacin da Bazoum ke shugabantar kasar.