Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana bacin rai tare da gargadin fitaccen malamin addinin musuluncin nan na kasar, Sheikh Ahmad Gumi, da ya daina tozarta ta da kalaman da ya jingina wa jami’an tsaro na taimaka wa ’yan bindiga.
Wannan gargadi na zuwa ne a matsayin martani ga kalaman da Sheikh Gumi ya yi na zargin cewa wasu daga cikin jami’an tsaro na tallafa wa ’yan bindiga wajen aikata barna a fadin kasar.
- 2023: Zan nemi shawarar tsayawa takarar shugaban kasa — Kauran Bauchi
- Maganin gargajiya ya yi ajalin mutum 10 ’yan gida daya
Yayin wata hirarsa da Gidan Talabijin na Arise a ranar Laraba, Sheikh Gumi ya yi zargin cewa wasu jami’an tsaro na hada baki da ’yan bindiga wajen aikata ta’asa ta sata da kashe-kashen mutane musamman a Arewa maso Yammacin kasar.
Sai dai yayin mayar da martani, Kakakin Rundunar Sojin Kasa na Najeriya, Birgediya-Janar Onyema Nwachuku, ya ce kamalan malamin wata manufa ce ta tozarta su da kuma nuna halin ko in kula dangane da yadda jami’anta ke sadaukar da rayukansu wajen kare martabar kasar a fagen daga.
A yayin da rundunar sojin ke shawartar al’umma da su kaucewa kalaman da ka iya ingiza ’yan bindigar su ci gaba da kai hare-hare da dagula al’amuran tsaro, Janar Nwachkwu ya ce irin wadannan kalamai ba su dace da wadanda ake kallo a matsayin jagororin al’umma ba.
“Wannan ikirari da malamin ya yi ya bata mana rai ba kadan kuma kira ne mai ban haushi wanda an yi shi da wata manufa ta tozarta mu da gan-gan gami da nuna halin ko in kula ga jami’anmu da suke sadaukar da rayukansu a kullum wajen kare martabar kasar nan da kuma tabbatar da wanzuwarta a matsayin kasa daya.
“Yana da muhimmaci jama’a su sani cewa, dakarun nan fa da ake zargi da hada baki da ’yan bindiga su din ne a kwanan nan suka sadaukar da tasu rayuwar wajen ceto daliban Makarantar Sakandiren Yawuri da ’yan bindiga suka sace a Jihar Kebbi.
“Da wannan muna kuma kira ga jama’ar kasar da su ci gaba da tallafawa ayyukan sojin ta hanyar samar da bayanai masu amfani domin inganta tsaro wanda a dole sai an hada hannu tare za a iya kawar da masu yi wa kasar nan zagon kasa.”