Tsohon Babban Hafsan Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya Laftanar-Janar Tukur Buratai mai ritaya ya ce halin da ya bar Rundunar ya fi yadda ya same ta inganci nesa ba kusa ba.
A jawabinsa yayin bikin faretin yi masa bankwana bayan ya mika ragamar Rundunar ga sabon Shugabanta, Manjo-Janar Ibrahim Attahiru, Buratai ya ce Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta samu dimbin nasarori a yaki da ta’addanci da sauran kalubalen tsaro a karkashin jagorancinsa.
- Kiris ya rage Obasanjo ya yi min ritaya shekaru 21 da suka wuce —Buratai
- Bidiyon Dala: Kotu ta sanya ranar ci gaba da shari’ar Ganduje
- Karin ’yan matan Chibok sun tsere daga hannun Boko Haram
- PDP ta bukaci Kotun ICC ta hukunta tsoffin Hafsoshin Tsaro
Ya ce shugabancinsa ya tabbatar da ganin cewa ta inganta jin dadin sojoji ta kuma ba su isasshen horo da kwasa-kwasai domin kara musu kwarewa a aikinsu na bakin daga.
“Yau ranar godiya ce ba ta lissafi ba, amma ina tabbatar da cewa halin da na bar Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ya fi yadda na same ta.
“A karkashin shugabancina Rundunar ta samu gagarumar nasara a yaki da ta’addanci a kasar nan.
“Muna fama da matsalolin tsaro daban-daban, amma yanzu ina fada da babbar murya cewa babu wani yankin Najeriya da ke hannun ’yan ta’adda ko masu miyagun laifuka.
“Duk da cewa yaki da ta’addanci na cikin gida bakon abu ne ga Najeriya, amma mun yi ta bijiro da hanyoyin dakile barazanar tsaron da ke bullowa a kasar.
“Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta kuma tsaya kai da fata wajen sauke nauyin da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya dora mata.
“Ina rokonku gaba da ku ci gaba da yin hakan,” inji Buratai a lokacin faretin bankwanan alfarmar da aka yi masa a Babban Barikin Soji na Mogadishu da ke unguwar Asokoro, Abuja.
Ya ce duk da cewa babu makawa wata rana sai an rabu da juna, ya rasa irin kalmomin da suka fi dacewa da zai yi amfani da su ya yi wa hazikan sojojin da jami’an Rundunar da suka yi aiki da shi bankwasa.
Bunkasa abubuwan more rayuwa
Ya ce Runduna ta kuma samu manyan nasarori ta bangaren ababen more rayuwa a fadin Najeriya.
Ya jinjina wa dakarun rundunar bisa yadda suka sadaukar da kai tare da cikakkiyar mubaya’a da suka taimaka wajen samun nasarorin da aka samu a karkashin shugabancinsa.
Tsohon Shugaban Rundunar Sojin Kasan ya yi godiya ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari saboda damar da kuma goyon bayan da ya ba shi domin kaiwa ga nasara.
Janar Buratari ya kara da yabo ga kokarin Gwamnatin Jihar Borno wajen yaki da ta’addanci, wanda ya ce cikin yardar Allah matsalar ta kusa zama tarihi.
Ya yi kira ga ’yan siyasa da su guji shigar da sojoji siyasa, sannan a matsayinsu na dattawan kasa ya kamata su ba wa sojoji goyon baya wajen kawo karshen matsalar tsaro.
Ya ce shigar da sojoji siyasa ba shi da riba, kuma cigaban kasa ba zai samu ba sai idan da tsaro, sannan shi kansa rashin cigaba yana haddasa rashin tsaro.
A jawabin nasa na bankwana, Buratai ya bukacin dakaru da ma’aikatan Rundunar da su ba da cikakken hadin kai da goyon baya ga sabon Shugaban Rundunar, Manjo-Janar Ibrahim Attahiru, domin a samu nasara a aikin da aka dora masa.