Jirgi dauke da sahun farko na maniyyata 378 daga Jihar Borno ya isa filin jirgi na Sarki Abdulaziz da ke Madina a kasar kasar Saudiyya.
Da misalin karf 2.15 kafin wayewar garin Litinin ne jirgin ya daga da maniyyatan, kamar yadda kula da walwala na hukuar jin dadin alhazan jihar, Mohammed Mainok, ya sanar.
Mainok ya kara da cewa ana sa ran kammala jigilar maniyyatan jihar su 1,818 a ranar ga watan June, 2024.
Don haka ya bukaci maniyyatan da su kasancewa wakilai na gari a Saudiyya da fatan za su yi aikin hajji karbabbe.
- An daure dan shekara 17 shekaru 14 a kurkuku saboda Fyade
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Haddasa Dambarwar Sarauta A Kano
“Su kasance masu bin dokokin Saudiyya tare da sanin cewa sun je kasar ne domin gudanar da daya daga cikin rukunan Musulunci guda biyar.
“Muna rokon su da su zaman wakilai na gari ga Jihar Borno da ma Najeriya a kasa mai tsarki,” in ji shi.