Wa’adin mulkin karamin lauje
’Yan hamayya sun dauje
Magabta ana kada musu jauje
Marasa kishi anai musu jaje
Muguwar manufa ta kuje
Masoya sun bararraje
Cikinsu har da mai saje
Suna kai-kawon a je-a je
Batutuwa ne a baje
A goge wa al’umma kaushin kauje
Butu-butun buruntun baza buje
Sai ai ta na-jan-je
Wai anje-anje
Ana ta bangaje-bangaje
Wasu har sun gwabje
Baba ya rataya gafaka
Sai fafutikar dinke baraka
Ko’ina sai ya taka
Al’umma dai ta ji a jika
Matakalar sabon salo aka taka
Iyakata dai kwatance
In yi ta zaro zance
Nagargaru kun san ayyukan dace
Kwararre ya zam fitacce
Babu waskiyar waskace-waskace
Rantsuwa ta ratsa
Miyagu sai a matsa
Masu himma a motsa
Ai gyaran karafunan tsatsa
Daukacin fagage a kutsa
Na ga jan cikin tsutsa
Masu hayagaga ban da nunin yatsa
Kar ku kitsa bahallatsa
Kowa dai ya samu tuwon datsa
Ai maganin ’yan dandatsa
Baba yai yunkurin aiki
Rikon ragama ba raki
Dattijo bai kukan aski
Ya dai yi furucin baki
Da karfinsa yake tattaki
Rantsuwar rikon ragama
Baba yai rummace
Kwado ne ba bambance-bambance
Ko ka-ce-na-ce
An tabbar da rikon makama
Da dai an ji jiki
Yanzu akwai karfin uwar-jiki
Sai dumfarar abin kirki
Banbamin bariki
Barden bindiga bai da burki
Rugumniyar rarumar ragama
Rahotannin rantsuwar raruma
Kar a ce Baba ya dan rurruma
Zangon karamin lauje ya kama
Mahukunta sun gyara zama
Fafatawa ba fantamawa
Tunkarar aiki ake takawa
Fafutikar farantawa
Al’umma su zam nunawa
Shugaba babu shakatawa
Ku kuwa
Gungun ’yan wawa
Lallai ana dada gargadawa
Dabarbarunku na dada birkicewa
Tuni an jinko damin da kuke tarawa
Saurayin-kirinki
Da an saki baki
Dagirgiri Dogari
Ya rage kai hari
Yanzu akwai rubirbidar na jaki
Baba a dage a ci maki
Garkamammun garada na shan tafkar tafki
Gundumin gwaramar gwabzar gwanki
’Yan kwadago na jiran taiki
Mangala ta antayo wa gayauna taki
Ayyukan ban mamaki
A daddale a harkokin mulki
Garken garakan naman girki
Gayaunar ganyayyaki
Tuwo miyar shukar shuwakar Shuwaki
Mu dai a kare mana mutunci
Tunda Baba ya hana cin hanci
Kishin kasa ya zam ba batanci
A kiyayi kulla munafunci
Sako-sakon sakacin sakarci
Kundumbalar kiyayya keke-da-keke
Karajin sarke-sarke
Kulle-kulle sun kuke
Kokiya ta harke
Kwakule-kwakulen hake-hake
Baban-burin-huriyya
Daga fari ka kai zuwa kurya
Kowace kwarya ta bi kwarya
A yasar da batun kiren karya
Talakawa sun yi juriya
Magabata na ta turjiya
Maketata na da kulle-kullen kulalliya
Munafukai na dada shirya murdiya
Mahankalata nai musu nuniya
Masana a sunce sasarin azargagiya
Rahotanin ruguntsumin ransuwar rugumniyar rarumar rakitar rikon ragama ya baibaye kafafen yada kakwazo na akwatunan baza batutuwa da masu wuntsila-gudi-gudin dodannin hotuna, wadanda suka kyallara wa Haurobiyawa da daukacin fadin duniya yadda Baban-burin-huriyya ya rungumi rikon ragamar al’umma a wa’adin mulki karo na karamin lauje.
A wajen dandazon kamun ludayin wa’adin mulki na karamin lauje, Baban-burin-huriyya da mataimakinsa Usainin-Babajo da daukacin mukarraban gwamnatinsa, sun hallara, illa dai kawai tasgaron taron rashin halartar su ‘O’o da ‘U’u, su Baba-Ojo mai gonakin Otawa da Gudun-loko da Jonatantin-mulki da sauran shagabanin al’ummar Haurobiya, wadanda suka yi fafutikar dawo da Jam’iyya mai danboto da sanda jirge kan karaga, amma hakar kwakwarensu ba ta cimma na kwadi ba, ballantana ma su da gama-garin ’yan barandarsu su yi ta kwankwada, har su kwalfe, su kwankwade a makwalwa kwat, ba tare da sun rage wa kowa ko dis ba.
Shin bayan lamushe zababbakar zabukan shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar kasa da Baban-burin-huriyya ya yi, ya kuma yi RUGUMNIYAR RARUMAR RAGAMAR RIKON RAKUMMAN jan akalar tafiyar da harkokin mulkin Haurobiyawa, mene ne ya rage a tunkara, musamman jin cewa wannan shi ne zangon karamin lauje na karkare wa’adin mulkinsa?
Amasar dai ita ce, tunda wa’adin mulkin karamin lauje ya sanya’yan hamayya sun dauje har magabta sun sha kidin juyin juya halin jauje, ga marasa kishi anai musu jaje, musamman jin cewa, muguwar manufarsu ta kuje. Don haka dai masoya aka bararraje har ma da Malam mai saje ana ta kai-kawo a je-a je; batutuwa ne dai a baje. Babban muradinmu dai, daidai kan wannan gabar ba ta wuce ganin an goge wa al’umma kaushin kauje ba.
Haurobiyawa, tare da daukacin ’yan makarantar Dodorido da ke falle shafukan mujallu da makalu da jaridu, har ma da masu koyon watsattsaken fallen shafukan wagagen littattafan DARUSSAN DUNGUN DUMUINIYAR DODANNIN DUNIYA, ina matukar son in ari bakunanku in cumuimiye, in tattaune muku albashe-bashe mai lunkumemen lawashin laushi. Bisa wannan dalili na kashin kaina, ni ina matukar son ganin an aiwatar da dimbin ayyukan alherin da aka tattauna, tare da kulla yarjejeniya kansu yayin da Baban-burin-huriyya ya yi SHELAR SHATALE-TALE SHAN SHAYI, tare da GANGANKON GWANGWANIN GAREWANIN GAHAWA; uwa-uba ina da muradin ganin kafuwar MAKEKIYAR MAKARANTAR MAMA, amma da sharadin ba za a yi mana farfajiyar koyi-ka-koyar ko koyi-ka-karkatar mai tsandarewar tsawwalar tsula tsadar tsilla-tsilla tsokale damar marasa galihu, har ta kai ga ’ya’yan ALARAMMAN ALMAJIRAN AREWATAWA ba za su iya kutsa kurungunsu ba; kuma ina nan da muradina na ganin kafuwar tsangayar alkafura da kundumbalar ninkayar iyo a kogin ilimu ta BABBAR BUKKAR BOKOKON BABAN-BURIN-HURIYYA, inda ’ya’yan Baba da Inna za su samu tarairaya da biyayya, bisa kumshiyar tanade-tanaden manhaja mara hajijiyar nusar da kyawawan ta’adun iyaye da kakanni. Lallai Baba ka tagaza, a agaza, musamman ma jin cewa Mama A’ISHATU FIL JAMI’A ta fita batun jar miya, ta samar wa su kolo da titibiri da gardin garada makoma a makarantarta, ko su ma sun dana SIRDIN SUDAN SADIDAN, su kuma rika kayatar da al’ummar Haurobiyawa tamfar dai sun fito daga kasaitattar kayatacciyar kasar Katar.
Mun dai karkare darasin wannan mako da neman agajin Mai-duka, Mai-kowa, Mai-komai don ya albarkaci wannan wa’adin karkare mulkin Baban-burin-huriyya, har mu samu mu kai ga gacin kawar da tashin-tashinar TSORO, har a fice daga yanayin nan na BA TSARO, SAI TSORO, tare da tabbacin cewa jami’an tsaro sun samu cikakken horon artabun angaje mana turka-turkar Haramta bobo da kwambon bokoko; a tarairayi ZULLUMIN ZALUNCIN ZALAMAR ZULLON ZINARUN ZAMAN-FARA; uwa-uba a tallafa wa Gwamna gwarangwam Mai-samari na Birnin Dikko, inda ba a dakon dakon mangalar aura, kan yadda zai tunkari matsalar KISISINAR KASHE-KASHEN KISSAR KISHIYOYIN KITSE-KITSEN KATSINTSINAWAR KASSARA al’umma. Yin haka ya zamo wajibi ganin cewa jihar da ake yiwa al’ummarta kisan mummuken sari-ka-noke ta Baba ce. Hasali ma har Magajin garin Daurama aka yi awon gaba da shi.
Lallai Baba ka kara daura damar, domin Jimamin jimirin jama’a na neman haifar musu da jante, amma dai da zarar an yunkura za a ci dunun darkakin dumuiniyar damuwar danniyar duniya. Mai-duka dai ya shige mana gaba a daukacin lamurranmu.