Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce yanzu mutane na ganin amfanin hikimarsa ta kulle iyakokin kasar.
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata, lokacin da yake jawabi a yayin bude sabuwar hedkwatar Hukumar Kwastam ta Kasa a Abuja.
- Annobar da ta fi COVID-19 na nan tafe – WHO
- ‘Akwai mata 332,000 da ke fama da yoyon fitsari a Najeriya’
An gina sabuwar hedkwatar ce a kan Naira biliyan 19.
A cewar Buhari irin wadancan manufofin na rufe iyakoki, za a jima ana cin moriyarsu, saboda kwalliya ta biya kudin sabulunsu.
Buhari, ya kuma ce hana shigo da shinkafa ’yar kasar waje na daya daga cikin irin makamantan matakan.
“Da gangan na rufe iyakokin tsandauri. Na ce ko dai kowa ya ci abin da muke nomawa, ko kuma mu noma abin da za mu ci. Daga bisani kuma mutane sun ga amfanin haka,” in ji Buhari.