✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rufe ‘boda’ ya kawo yunwa da rashin aiki a Arewa —CNG

Ƙungiyar ta bayyana cewa ci gaba da rufe iyakar Najeriya na kan tudu yana amfanar da yankin Kudu tare da rusa tattalin arzikin Arewa.

Gamayyar Ƙungiyoyin Arewacin Najeriya (CNG) ta soki ci gaba da rufe iyakar ƙasar na kan tudu, lamarin da ta bayyana cewa yana amfanar da yankin Kudu tare da cutar da Arewa.

Ƙungiyar CNG Reshen Jihar Taraba ce ta bayyana haka, tana mai zargin cewa Shugaba Tinubu ya tsara sabuwar dokar haraji da ya ɓullo da ita ne da nufin ya amfani yankin Kudu.

Sanarwar da kungiyar ta fitar hannun Kodinetan ta na Jihar Taraba, Kwamred Idris Ayuba, ta ce dora laifin yawancin matsalolin da Arewa ke fama da su a kan tsare-tsaren Gwamnatin Tinubu.

Kwamred Idris Ayuba ya ce, “cire tallafin mai da rufe iyakar Najeriya ta kan tudu da sabuwar dokar haraji, kaɗan ne daga cikin tsare-tsaren da suke jefa yankin Arewa cikin matsaloli, duk daga lokacin da wannan gwamnati ta hau mulki.”

“Raguwar amfani da fetur sakamakon cire tallafi ba abin ƙwarai ba ne, alama ce ta raunin harkokin tattalin arziki da ya rage ƙarfin ’yan ƙasa na iya amfani da makamashi,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, “rufe iyaka ya karya ’yan kasuwa musamman ’yan tireda da dama a Arewa, lamarin da ya kawo ƙaruwar talauci da rashin aikin yi a yankin.

“Tsarin ya amfani yankin Kudu, inda ya kara buƙatar sayen kayan da aka sarrafawa a yankin, wanda hakan ke bunkasa tattalin arzikinsu.

“Ga shi kuma yankin Kudun yana mai karin kuɗaɗen shiga daga haraji da kuma kudin fiton kayan da ke shigowa daga ƙetare.

“Rufe bodan ya kawo rashin adalci a fannin rabon tattalin arziki, ta yadda yankin Kudu ke amfana da tashoshin jiragen da iyakoki da hanyoyin shigowa Najeriya, wanda hakan ya sa harkokin tattalin arziki suka tattara a can, amma ya mayar da yankin Arewa kurar baya,” a cewar Idris.

Ya bayyana cewa babbar illar da rufe iyakar kan tudu ta yi wa Arewa shi ne ɓangaren kasuwancin ƙasa da ƙasa, wanda a cewarsa ya dogara ne a kan harkokin da ake yi ta iyakokin kan tudu tsakanin ƙasashe masu maƙwabtaka da juna.

Wannan, a cewarsa ya gurgunta harkokin tattalin arziki da kuɗaɗen shiga a Arewa, hakazalika a sabuwar dokar harajin da Tinubu ya ɓullo da ita.