A yayin da Lionel Messi ya zama Gwarzon Dan Kwallon Duniya na bana, shi kuwa Cristiano Ronaldo ya zama Gwarzon Dan Kwallon Italiya ne.
A ranar Litinin da ta gabata ce kulob din Jubentus na Italiya ya zabi Cristiano Ronaldo a matsayin Gwarzon Dan Kwallon kulob din a bana. An yi bikin ne a ranar Litinin a Milan da ke Italiya a daidai lokacin da ake bikin Gwarzon Dan Kwallon Duniya a Faransa.
Bikin karrama Ronaldo ne ya hana shi halartar wanda aka gudanar a Faransa, inda ya nuna bikin Magaji bai hana na Magajiya.
Kafin wannan lokaci Messi da Ronaldo suna kan-kan-kan wajen lashe kyautar Gwarzon Dan Kwallon Duniya sau biyar-biyar amma yanzu Messi ya yi masa zarra bayan ya lashe ta shida.
Ronaldo a bara ya taimaki kulob din Jubentus wajen lashe kofunan Serie A da na kalubale a kakar wasansa ta farko bayan ya canja sheka daga Real Madrid na Spain.
Ronaldo ne na uku a jerin ’yan kwallon da suka fafata a gasar Gwarzon Dan Kwallon Duniya ta bana ta Ballon D’or.