Dan wasan gaba na Manchester United da Portugal, Cristiano Ronaldo, ya kafa tarihin zama dan wasan da ya fi kowanne yawan jefa kwallaye a wasannin kwallo na duniya.
Cristiano Ronaldo mai shekaru 37 ne ya ci dukkannin kwallaye 3 a wasan da Manchester United ta lallasa Tottenham da ci 3 da 2 a daren Asabar, lamarin da ya sa har yanzu United ke da kwarin gwiwar kasancewa a cikin kungiyoyi 4 na saman teburin gasar Firimiyar Ingila.
- Mustafa Shehu: Mutumin Kano da ya zama Shugaban Kungiyar Injiniyoyi ta Duniya
- Ban fita daga PDP ba tukunna —Kwankwaso
Kwallo ta biyu da Ronaldo ya ci wa United ce kwallonsa ta 806 a sana’arsa ta kwallon kafa, kuma ita ce ta sanya shi ya zama kan gaba a hukumance a wajen cin kwallaye a duniya.
Ana saura minti 10 a tashi wasa ne dan wasan na kasar Portugal ya saka wata kwallo da kai, wadda ita ce kwallonsa ta 807.
Bayan saka wannan kwallo a raga ce aka sauya Ronaldo, wanda magoya baya suka mike tsaye, su na masa jinjina a yayin da yake barin filin wasa.
Tuni dai Ronaldo ya zarce wadannan ‘yan wasa a wajen yawan kwallaye: J. Bican 805, Romario 772, Pele 767 da Messi 759.