Alamu sun kara bayyana cewa Cristiano Ronaldo zai yi bankwana da kulob dinsa na Juventus.
A daren Laraba wani bidiyo ya nuna wata motar dakon kayan wani kamfanin da ke Lisbon ta bi dare tana daukar motocinsa na alfarma ciki har da Bugatti da Jif din Marsandi da Maseratti.
An wallafa bidiyon safarar motocin Ronaldon da aka yi cikin dare a wani shafin intanet na kwallon kafan Italiya mai suna Per Sempre Calcio.
Da alama an dauki bidiyon ne daga kan wani bene da ke kusa da garejin da dan wasan ya ajiye motocin a birnin Turin.
Kamfanin Rordo Cargo, wanda ya yi dakon motocin a Lisbon babban birnin Portugal ya shahara wajen jigilar motocin alfarma na ’yan wasan kwallon kafa a duniya.
Wani da ake zargin makwabcin Ronaldon ne mai suna Luciano Saroglia, shi ya tsegunta wa wani shirin musamman kan wasanni abin da ya gani.
Da yake magana da gidan Rediyon Punto Nuovo, Luciano ya ce: “Kasancewata haifaffen birnin Turin, kulob din da nake goya wa baya kawai shi ne Juventus.
“Shekara uku da suka gabata lokacin da Ronaldo ya zo nan, wasu motocin dakon kaya guda biyu sun sauke motocinsa inda aka shigar da su garejin, kuma na shaida hakan,’’ inji makwabcin nasa.
Wasu rahotani sun ce Ronaldo na fuskantar kyama daga abokan wasansa a kulob din Juventus, wadanda suke kwafar yadda daraktocin kulob din ke daukar dan wasan a zaman dan shalelensu.
Ko a makon jiya, sai da aka kara wa ’yan wasan kulob din lokacin atisaye na kwana guda a daidai lokacin da Ronaldon yake wani bulaguro zuwa hedikwatar kamfanin kera motocin Ferrari da ke kusa da Bologna a Italiyar.
Sannan akwai batun rashin tabuka abin a zo a gani da Juventus din ta yi duk da ta ci kofin Coppa Italia a ranar Laraba; Akwai kuma yiwuwar kulob din ya gaza samun gurbin shiga wasannin Zakarun Turai na kaka mai zuwa.
Hakan zai faru ne idan har Napoli da ke gaban Juventus din a teburin Serie A ta ci wasanta na karshe da Verona a ranar Lahadin nan; koda kuwa Juventus din ta lashe wasanta na karshe da Bologna.
Tsohon dan wasan Manchester United da Real Madrid din ya koma Juventus ne a 2018, har yanzu yana da sauran shekara guda a kwantiragin da ya rattaba hannu inda ake biyan sa Yuro dubu 540 duk mako.